Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) za ta yi zaman gaggawa domin lalubo yadda za a shawon kan kungiyoyin kwadago su fasa shiga yajin aiki da zanga-zangar da suke shirin farawa.
Idan za a iya tunawa, kungiyar kwadago ta NLC ta yi barazanar fara yajin aiki da zanga-zanga a fadin Najeriya idan Gwamnatin Tarayya ba ta janye karin farashin man fetur da wutar lantarki da aka yi ba.
- Shugaban Sojin Sama ya auri Minista Sadiya Umar-Farouq
- Ambaliya ta ci mutum 5 da rabin gari a Jigawa
Darakta-Janar na NGF Asishana Okauru, ya ce ana sa ran dukkannin gwamnoni za su halarci zaman na ranar Alhamis saboda girmar matsalar da ke butakar a gaggauta shawo kanta domin kauce wa kara tsanantar matsalolin da ake ciki a yanayin COVID-19.
- Gwamnati na neman sulhu
A hannu guda kuma, Gwamnatin Tarayya na shirin tattaunawa da kungiyoyin kwadago a ranar ta Alhamis kan barazanar da kuniyoyin suka yi.
Sanarwar da Ma’aikatar Kwadago ta Kasa ta fitar ranar Laraba ta ce gwamnati za ta sanar da tallafi da za ta bayar domin rage radadin da karin farashin a kan ma’aikata.
Ma’aikatar ta ce Minista, Chris Ngige zai jagoranci bangaren gwamnati a zaman da za a yi da misalin karfe 3.00 na rana a Fadar Shugaban Kasa.
A baya tattaunawar bangarorin biyu ya kasa cimma matsaya saboda gwamnati ta ki amsa bukatar NLC na janye karin farashin da kuma ba wa ma’aikata tallafi.