✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: Gwamnatin Tarayya ta maka likitoci a kotu

Ministan ya ce likitocin sun yi gajen hakuri kan yarjejeniyarsu da gwamnati.

Gwamnatin Tarayya ta maka Kungiyar Likitoci Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) a gaban Kotun Masana’antu don yanke musu hukuncin da ya dace a kan yajin aiki da suke gudanarwa a halin yanzu.

Ministan Kwadago, Chris Ngige, wanda ya shigar da karar a gaban kotun a ranar Alhamis, ya bukaci kungiyar da ta sanar da mambobinta da ke yajin aiki irin kokarin da gwamnati take yi na kawo karshen lamarin.

– Matsalar tsaro: Buhari ya nuna damuwarsa
Ambaliyar ruwa: Mutum 13 da gidaje 1,600 sun hallaka a Bauchi

Ya kuma yi barazanar cewa gwamnati za ta tilasta dabbaka rashin biyan albashi idan ba su yi aiki ba.

Ministan, ya bayyana cewa kotun ta karbi takardar karar da ya gabatar a kan lamarin a gabanta tare da Hukumar Lafiya ta Kasa.

Wani bangare na sanarwar da Ngige ya rattaba wa hannu ya ce, “Ganin cewa takaddama ta ki karewa tsakanin kungiyar likitoci ta NARD da Gwamnatin Tarayya, ana ta neman mafita amma abun ya ci tura.

“Idan aka lura, yajin aiki da suka tsunduma a halin yanzu ya saba doka, saboda a baya an kulla yarjejeniya da su kan yadda Gwamnatin Tarayya za ta cika alkawuran da ta daukar musu, amma sun kasa hakurin har hakan ta samu.

“Don haka, yanzu na yi amfani da karfin iko na gabatar da lamarin a gaban kotun don nemo mafita dangane da wannan tirka-tirka.”