Gwamnatin tarayyar Najeriya da Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ASUU sun yi tattaunawar kulla yarjejeniya ranar Litinin akan yajin aikin gama gari da kungiyar take yi.
Ministan qwadago na Najeriya Sanata Chris Ngige ne ya jagoranci tattaunawar da aka yi a Abuja.
Ngigie ya ce, sun kai karshen yarjejeniyarsu tsakaninsu da kungiyar ASUU, Gwamnatin tarayya baiwa kungiyar ASUU Naira biliyan 15.4 don kungiyar ta samu damar biyan albashi ma’aikata, wanda ya na daya daga cikin bukatun kungiyar.