Gwamantin Tarayya na shirin hawa taburin tattaunawa da likitoci a ranar Laraba, yayin da kungiyar likotici ta NARD ke shirin fara yajin aiki a ranar Alhamis.
Ministan Kwadago, Chris Ngige ta bakin kakakinsa, Charles Akpan, ya aika wa Aminiya goron gayyatar zuwa zaman tattaunawar a Hedikwatar Ma’aikatar da ke Abuja, da misalin karfe uku na rana.
- An kama masu yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
- Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi
- Shin malaman Kano za su iya ja da Abduljabbar?
Ngige zai jagoranci bangaren gwamnati a zaman, yayin da Shugaban NARD na kasa, Uyilawa Okhuaihesuyi zai jagornaci daya bangaren.
Bayan bullar cutar COVID-19 a karo na biyu ne likitocin suka fara barazanar tafiya yajin aikin sai abin da hali ya yi, daga ranar 1 ga Afrilu, 2021, matukar gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba.
Likitocin na bukatar a biya duk bashin da suke bi na albashi da kuma hakkokin abokan aikinsu da suka rasu a yayin aikin yaki da COVID-19
Suna kuma son a kara yawan alawus din da ake biyan su na yaki da COVID-19 zuwa kashi 50 na tsurar albashinsu.
Baya ga haka, a biya su bashin duk alawus-alawus dinsu na aiki yaki da cutar, musamman a manyan cibiyoyin lafiya.
Buhari zai gina asibitin zamani a Abuja
Kafin tafiyar Shugaba Buhari kasar waje ranar Talata domin duba lafiyarsa, Fadar Shugaban Kasa ta ce gwamnati na kan tattaunawa da likitocin da ke barazanar shiga yajin aiki.
“Gwamnati na kan tattaunawa da su kuma na tabbata Ministan Kwadago ya san abin da ya kamata saboda kwararre ne a fannin. Sanata Ngige na kula da wannan,” inji kakin Shugaban Kasa, Garba Shehu.
Garba Shehu, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa gwamnati za a gina asibitin da zai yi gogayya da kowanne a duniya a Abuja.