✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aiki: Daliban jami’a miliyan 2 na zaman dirshan a Birtaniya

Yajin aikin ya fara tasiri kan harkokin gwamnati wanda hakan babban kalubale ga tattalin arzikin kasar.

Rahotanni daga kasar Birtaniya sun bayyana cewa kimanin daliban jami’a miliyan 2.5 ne ke zaune a gida bayan da malamansu suka shiga yajin aiki.

A ranar Alhamis ce malaman suka fara yajin aikin a matsayin wani mataki na neman karin albashi daga wajen gwamnatin kasar.

Tuni da ma ma’aikatan lafiya da na gidan waya da lauyoyi da malaman kananan makarantu da sauransu suka shiga yajin aiki a kasar ta Birtaniya.

Baki dayan ma’aikatan sun tsunduma yajin aikin ne saboda tsadar rayuwar da kasar ke fuskanta, wanda haka ya sa suke bukatar gwamnati ta yi musu karin albashi don cimma daidaito.

Tuni yajin aikin ya fara tasiri kan harkokin gwamnatin wanda hakan wani babban kalubale ne ga tattalin arzikin kasar.

Wannan shi ne makamancin abin da ya faru a Najeriya inda Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) a kasar ta shafe wata takwas tana yajin aiki don neman cimma bukatunta a wajen gwamnati.