✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin aiki: ASUU ta lashi takobin hukunta jami’o’in da suka bijire mata

Kungiyarta ce za ta hukunta jami'o'in da suka bijire mata

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta yi barazanar daukar mataki kan duk jami’ar da ta yi kunnen uwar shegu da umarnin da ta bayar na ci gaba da yajin aiki, yayin da take tattaunawa da gwamnati kan bukatunta.

Shugaban Kungiyar na kasa, Farfesa Osodeke ne ya bayyana hakan ga manema labarai Abuja, in da ya ce za su tabbatar da daukar mataki kan wadanda suka yi biris da umarnin kungiyar.

Shugaban ya ce tuni ma sun riga sun fara aika takardar neman bahasi ga wadanda suka aikata hakan kamar dai yadda yake a dokar kungiyar.

Ya kuma ce tun lokacin da kungiyar ta zauna a taron tattaunawar da Shugaban Ma’aikata ya kira su kimanin wata guda da ya gabata, gwamnati ba ta sake tuntubar su ba, sai dai ya ce za su sake shiga wani taron tattaunawar nan da sati guda.

Idan za a iya tunawa, kimanin wata biyar ke nan kungiyar ta shafe tana gudanar da yajin aiki, bisa kin biya mata bukatunta, da kuma cika musu alkawuran da gwamnati tayi tun a 2009.

Aminya dai ta gano cewa wasu daga cikin jami’o’in kasar nan irinsu Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ibadan tuni sun koma bakin aiki duk da umarnin kungiyar.