✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin aiki: ASUU ta caccaki dalibai kan juya mata baya

Shugaban ASUU yi wa Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) tatas kan sukar yajin aikin malaman jami'a

Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ta yi wa Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) wankin babban bargo kan rashin goyon bayan yajin aikin da malaman ke gudanarwa.

A martaninsa ga matakin na NANS, Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osedeke, ya ce kungiyarsa ba ta nemi goyon bayan dalibai ba kafin ta fara fafutikar da take yi.

Ya yi wannan jawabi ne bayan Shugaban NANS, Sunday Asefon, ya yi zargin son zuciya a yajin aikin da ASUU ke yi, don haka ya ce babu ruwan dalibai kuma ba za su su sanya baki a takaddamar ba.

Osedeke ya yi raddin ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, yana mai cewa daliban da ke zaune a gida saboda yajin aikin ba su taimaka wa ASUU da komai a fafutikar da take yi domin su ba.

Ya ce, “Daga lokacin da iyaye da dalibai suka karbi ragamar wannan fafutikar da muke yi, to ba za a kara samun wannan mastala ba.”

Amma ya ce, “Shin [NANS] sun taba mara wa fafutikarmu baya, in banda bin mutane ofis-ofis? A bar wannan batu.  Amma, a je a tambayi gama garin dalibai, ba wadannan shugabannin kungiyarsu ba.

“Wai me muke nema ne? Shin jami’o’in kasar nan suna da inganci? Makarantun firamare da sakandare na gwamnati sun mutu, amma malamansu ba su tashi sun yaki matsalar ba.

“Yanzu haka kaso 99 cikin 100 na dalibai a jami’o’in gwamnati suke karatu, amma daliban wai a ce su daliban za su budi baki su ce mana ‘ba ma goyon bayanku.’ To mun nemi taimakonsu ne kafin mu fara?”