✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yajin Aiki: ASUP ta bai wa Gwamnati wa’adin kwana 14

A biya mana bukatunmu ko kuma mamabobinmu su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

Kungiyar Malaman Kwalejojin Fasaha (ASUP), ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni biyu a kan ta biya mata bukatunta ko kuma mamabobinta su tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.

ASUP ta cin ma wannan matsaya ne bayan taron da Majalisar Zartawar kungiyar ta gudanar karkashin jagorancin shugabanta na kasa, Kwamared Anderson  Uzeibe, a ranar 11 ga Mayun 2022, inda suka yanke shawarar shiga yajin aiki muddin Gwamnatin ta gaza wajen cin ma bukatunsu bayan kwana 14.

Bukatu guda tara ne ASUP ke nema Gwamnati ta cika mata su, ciki har da neman a mika mata biliyan N15 wanda Shugaba Buhari ya amince a ba ta tun watanni 11 da suka gabata don tada komadar kwalejojin fasaha mallakar gwamnati a fadin kasa.

Sauran bukatun sun hada da biyan kukaden basussuka da ake cewa ariyas na sabon tsarin albashi mafi karanci ga mambobinta da neman a sako mata sabon jadawalin ayyukan makarantun wanda aka amince da shi tun a 2017 da gaggauta aiwatar da sabon tasarin albashi da shekarar ritaya ga ma’aikatan makarantun da sauransu.

Kazalika, ASUP ta bukaci jama’ar kasa da su nunar wa gwamnati bukatar da ke akwai ta hanzarta biya mata bukatunta don kauce wa rufe makarantun da ke karkashinta a fadin kasa.