dan kwallon kungiyar kwallon kafa ta U-20 ta Najeriya Musa Yahaya yanzu haka yana haskakawa a kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 21 a kulob din Tottenham da ke Ingila tun bayan da kulob din ya saye shi a farkon shekarar nan da muke ciki.
dan kwallon, wanda ya taba yin wasa a kulob din Mutunchi Academy da ke Kaduna ya fada wa kafar sadarwar AfricanFootball.com cewa yanzu haka ya zura kwallaye hudu daga cikin wasanni bakwai da ya yi. Ya kara da cewa: “Na yi farin ciki da kulob din ya ba ni dama na yi atisaye a babban kungiyar kwallon kafa ta Tottenham da hakan ke nuna da cewa na kusa fara yin wasa a matakin manya”, inji shi.
Ya ce yana sa ran ziyartar Najeriya a watan Oktobar bana a lokacin da zai samu gajeren hutu.
Yana daga cikin ’yan kwallon da Hukumar NFF ta daga martabarsu zuwa ta U-20 daga U-17 bayan da suka lashe gasar cin kofin duniya na matasa.
Ana sa ran zai fara yin wasa a matakin manya a kungiyar kwallon kafa ta Tottenham a shekara mai zuwa a lokacin da zai cika shekara 18.