✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Zulum ya halarci jana’izar manoma 43 da aka yi wa yankan Rago

Gwamnan ya halarci sallar jana'izar da aka yi inda ya taimaka wajen birne manoma 43.

A ranar Lahadi, Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya halarci sallar jana’izar manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan Rago.

Aminiya ta ruwaito cewa a Asabar din da ta gabata ne mayakan suka yi wa akalla manoma 40 dirar mikiya a gonaki, suka daddaure su, suna yankawa a kauyen Koshobe, da ke Zabarmari, Karamar Hukumar Jere.

Gwamna Zulum yayin da ake sallar jana’iza
Zulum yana taimakawa wajen ajiye gawa
Gawarwakin Mutane 43 da aka yiwa yankan Rago
Gawarwakin Mutane 43 da aka yiwa yankan Rago