✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zazzabin Lassa ke hallaka mutane a jihohi

Ya hallaka mutum 16 a Ondo, likitoci 3 a Kano Likitoci biyu da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano…

  • Ya hallaka mutum 16 a Ondo, likitoci 3 a Kano

Likitoci biyu da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano da wata mai ciki sun rasa rayukansu sakamkaon kamuwa da cutar zazzabin Lassa da suka yi, bayan da ake fargabar sun kamu da zazzabin ne lokacin da suka gudanar da tiyatar haihuwa ga wata mai cikin; wacce ta dawo daga Jihar Bauchi don ziyarar ’yan uwanta.

A Jihar Ondo kuwa, gwamnatin jihar ta ba da tabbacin bullar zazzabin Lassa, inda aka tabbatar da ya hallaka mutum16.

Likitocin da suka rasu a Kano, sun hada da Dokta UmmulKuthum Abba da Dokta Habibu Musa.

Majiyar Aminiya ta ce bullar cutar ta faru ne sakamakon wata mata mai kimanin shekara 28 wacce ke Unguwar Gwale da ta kamu da rashin lafiya mako biyu bayan rasuwar mahaifiyarta. Wadancan likitoci biyu da suka rasu ne suka yi mata aikin fitar mata da da daga ciki.

A cikin sakon waya da Jami’ar Hulda da Jama’a ta Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, Hauwa Abdullahi ta aiko wa Aminiya, ta ce tuni asibitin ya fara binciken yiwuwar samun bullar cutar zazzabin Lassa a jihar, wanda haka ya janyo aka tura samfurin kwayar cutar ga Cibiyar Dakile Cututtuka ta Kasa don gano gaskiyar lamarin.

Gwamnatin Jihar Kano, ta bakin Kwamishinan Lafiya, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa, ta bayyana cewa tun daga lokacin da suka samu labarin barkewar cutar daga Asibitin Koyarwa na Malam Aminu, inda aka samu mutum uku da suka kamu da cutar, ma’aikatar ta dauki matakan gaggawa don dakile yaduwarta a tsakanin al’ummar jihar.

“Bayan mun samu cikakken rahoto daga Hukumar Gudanar da Aune-Aune da ke Abuja, wanda ya tabbatar da cewa mutum biyu sun kamu da wanann cuta ta Lassa, sai Gwamnatin Jihar Kano ta dauki matakai. Na farko, ta sake bude cibiyar da ake kebance masu wata lalura ta musamman a garin ’Yargaya da ke jihar. Na biyu, an kuma dawo da ayarin jami’an lafiya na masu ba da agajin gaggawa (RRT). Haka kuma an gudanar da taron gaggawa don neman hanyoyin shawo kan cutar da samar da magunguna don taimakon gaggawa.

A Jihar Ondo, bayan ga samun rahoton tabbacin rasuwar kimanin mutum 16, gwamnatin jihar kuma ta tabbatar da cewa an samu mutum 86 da ke dauke da cutar ta Lassa, tun shigowar sabuwar shekarar nan. An samu bullar cutar a yankunan kananan hukumomin Owo da Kudu maso Yamma na Akoko da Kudancin Akure da kuma Ondo ta Yamma.

Jami’in kula da cututtuka na musamman a Jihar Ondo, Mista Steben Fagbemi, ya tabbatar da haka a ranar Talatar da ta gabata, bayan kammala taro da Gwamna Rotimi Akuredolu ya yi da mukarraban gwamnatinsa.

Fagbemi ya bayyana cewa sai da cutar ta ci karfin majinyatan, kafin a kai su asibitoci domin magani. Ya ce a yanzu haka akwai majinyata 47 da ke amsar magani kuma da alamar suna samun sauki. Kazalika, ya ce an sallami majinyata 21 da suka warke daga cutar ta Lassa.

Da yake karin bayani game da cutar a Jihar Kano, Kwamishinan Lafiya, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa cewa ya yi a yanzu haka Gwamnatin ta killace mutum daya tare da sanya kimanin mutum 292 a cikin jerin wadanda gwamnatin ke lura da su, tare da yi musu gwaje-gwaje don gano ko sun kamu da wannan cuta, sakamakon haduwa da wadancan mutane da suka kamu da cutar da farko, wadanda kuma suka rasu.

A cewar Kwamishinan, baya ga daukar wadannan matakan, a gefe guda kuma gwamnatin ta dauki matakan wayar da kan jama’a kan bullar cutar, inda za ta hada kai da shugabannin al’umma da na addini don wayar da kan mutane a masallatai da kuma sanya sanarwa a kafafen watsa labarai da kuma wayar wa jami’an lafiya kai da kuma samar dakayan aiki don kai daukin gaggawa.

Har ila yau gwamnatin ta yi kira ga al’ummar jihar su dauki matakan wanke hannuwa a koyaushe tare da kula da tsabtar muhallinsu da kuma guje wa haduwa da dabbobin daji da kuma cin naman da bai dahu sosai ba da kuma kaurace wa haduwa da mutanen da suka kamu da cutar ko  suka hadu da wadanda suka kamu da cutar.

Haka kuma ya ce akwai bukatar a yi gaggawar zuwa asibiti da zarar an ji wani zazzabi mai zafi.

Dokta Ibrahim Musa, likita ne a bangaren  kiwon lafiyar da ya danganci jini a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano, ya ce ana kamuwa da zazzabin Lassa ne sakamakon wani nau’in bera da ke dauke da kwayar cutar.

“Idan ya kasance irin wannan bera ya taba wani abu, musamman abinci, sanann mutum ya zo ya taba, to akwai yiwuwar ya kamu da wannan cuta. Haka idan mutum ya yi wata mu’amala ta gaisawa ko taba jikin mai cutar ko yin amfani da kayayyaki guda kamar cokali ko ban-daki; to nan ma akwai yiwuwar a kamu da cutar.

“Sai kuma wata hanya wacce ta shafi daukar kwayar cutar ta hanyar iska, ma’ana idan iska ta kwaso busashen jini ko yawu da sauransu. Sai dai wannan hanyar ba a fiye kamuwa da cutar ba,” inji Dokta Musa.

Dokta Musa ya bayyana hanyoyin da mutane za su bi wajen kare kansu daga kamuwa da cutar, inda ya ce akwai bukatar mutane su kasance cikin tsabta, ta hanyar wanke hannayensu da kuma kula da muhallinsu.

“Tsabta ita ce babbar hanyar kare kai daga kamuwa da cutar. Sannan da guje wa yin mu’amala da masu cutar ko wadanda ke da alamun yiwuwar kamuwa da cutar. Haka kuma su ma jami’an lafiya, akwai bukatar su kula wajen kula da masu cutar ta hanyar amfani da kayayyakin kariya. Wato su rika sanya rigar likita da safar hannu da takunkumi a baki da wanke hannu da magani da sauran matakan kariya,” inji shi.

Baya ga jihohin Kano da Ondo, zuwa yanzu zazzabin Lassa ya bulla jihohin Enugu da Delta da Edo da Bauchi da sauransu.

A Delta, an samu rahoton mutuwar mace daya, inda wani mutum kuma yake jinya. Gwamnatin jihar ta ce matar ta rasu ne a Asibitin Gwamnatin Tarayya da ke Asaba. Kamar yadda Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dokta Mordi Omonye ya tabbatar. Ya ce, matar ta rasu ne kafin a ba ta magani, kwana daya da kai ta asibiti. Ya ce shi kuwa daya majinyacin, dan hidimar kasa ne kuma an kai shi asibitin ne a ranar Lahadin da ta gabata, kafin daga bisani aka mai da shi Asibitin Kwararru na Irrua da ke Jihar Edo.

A Jihar Enugu ma an samu rahoton mutuwar mutum daya a ranar Talata da ta gabata a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Kimiyya da Kere-Kere da ke Parklane. Haka kuma an dauki matakan bincike na asalin yadda mamacin ya kamu da cutar.

A Jihar Bauchi ma an samu rahoton bullar cutar. A tattaunawa da wakilinmu ya yi da Babban Sakataren Cibiyar Kiwon Lafiya a Jihar Bauchi, Dokta Rilwanu Muhammad ta waya, ya ce tun mako uku da suka gabata ne aka samu rahoton da ke zargin bullar cutar ta Lassa a jihar. Sai dai ya bukaci a ba shi lokaci domin ya tantance bayanan da ke akwai domin sanar da al’umma abin da ake ciki.

“Ba zan iya ba ka tabbacin cewa cutar Lassa ce ta barke ba a yanzu, domin na yi tafiya wajen Najeriya lokacin da aka samu rahoton zazzabin. Ba ni da masaniyar cewa ko binciken da aka yi ya tabbatar da cewa Lassa ce ko akasinta. Ka zo ofis gobe domin ka samu sahihin bayani,” inji Dokta Rilwanu.

A Jihar Ebonyi ma cutar ta bulla, inda aka samu rahoton rasuwar mutum guda, kamar yadda Aminiya ta kalato. Kwamishinan Lafiya na Jihar Ebonyi, Dokta Daniel Umezurike, ya ta’allaka rasuwar majinyacin kan jinkirin kai rahoto ga hukumomin lafiya na jihar a kan lokaci. Ya ce zuwa yanzu an sake bude asibitin da aka yi wa mamacin jinya, bayan rufe shi da aka yi kwanakin baya.

Jihar Ebonyi, ita ce kan gaba da cutar ta Lassa ta yi wa illa a shekarar 2005, inda sama da mutum 20 suka rasa ransu.