✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda zanga-zangar damar mallakar bindiga ta karade Amurka baki daya

Wani hari da aka kai a wata makaranta a Parkland da ke birnin Florida wanda aka kashe kimanin mutum 17, ya haifar da wata zanga-zanga…

Wani hari da aka kai a wata makaranta a Parkland da ke birnin Florida wanda aka kashe kimanin mutum 17, ya haifar da wata zanga-zanga a manyan birane da ke cikin Amurka da ma fadar Gwamnatin Amurka wacce ake kira White House.

Masu zanga-zangar dai suna kira ne da a samar da wata dokar da za ta lura da mallakar bindiga barkatai idan har ba za a hana mallakarta ba dungurungun.

Bayan wannan zanga-zangar ne kuma, kwatsam sai ga wasu su kuma sun shirya wata zanga-zangar kishiyar ta farkon suna kira da gwamnati da kada ta sake ta dubi wannan batu na yin dokar hana mallakar bindiga ballantana ma har ta yi wa dokar wani kwaskwarima.

Masu wannan zanga-zangar sun shirya gudanar da wanna zanga-zangar ne a duk fadin majilisun dokokin  Amurka, wanda ba zai rasa nasaba da ganin cewa kowace jihar na Amurka na iya yi wa kanta dokar da ya dace da ita ne.

Da yawan masu wannan zanga-zangar sun taru ne a gaban kofar majilisar dokokin jihohinsu da ma majilisar dokoki na tarayya, wasunsu dauke da bindiga.

Abin da ko suke nema a yi shi ne kada a samar da wata dokar da za ta kawo matsala wajen mallakar bindiga suna cewa wannan ya take musu hakkinsu na ‘yan kasa.

Misali wadanda suka gudanar da wannan zanga-zangar a Jihar Daleware sun yi cincirindo a gaban kotun kolin jihar suna gabatar da jawabai tsakaninsu. Wstley Williams daya daga cikn masu zanga-zangar da ya yi wa taron jawabi dauke da bindigarsa yana cewa muddin aka fara taba dokar mallakar bindiga to watarana ma za a ce ne an hana mallakar bindigar dungurungum, ya ci gaba da cewa kamar kana daki ne sai ka rika cire bulo guda kullun, wata rana sai ka wayi gari ba ginin gaba dayansa.

Shi ma Dabe Gulya daya daga cikin wadanda suke shirya zanga-zangar a birnin Augusta da ke Jihar Maine ya ce mutane kusan 800 ne suka fito domin halartar wannan gangamin kuma  kusan duk wanda ya mallaki bindiga mutun ne mai bin doka da oda.

Kusan daukacin wadanda suka halarci irin wannan gangamin a birnin Atlanta ko suna dauke da bindiga da kuma tuta da ke da rubutun “ban yarda a yi wasa da damar da nake da ita ba’’

Da yawan mahalarta wannan gangamin suka ce duk da yake ba su kai yawan wadanda suka gudanar da kwatankwancin irinsa ba, amma  suna da wakilcin mutane daga kowane sassa a duk fadin Amurka.

Suka ce za su yi duk abin da za su iya yi ga duk wata majilisar jiha ko ta tarayyar da ta yi yunkurin taba dokar hana mallakar bindiga ga ’yan kasa domin ’yancinsu ne.