Ayuba Muhammad dan kasuwa ne mai shekara 35 a Kano da yake aikin wakilin bankin First City Monument Bank (FCMB). A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana yadda ya bar aiki a wani kamfani ya fara sana’ar POS, da kuma yadda sana’ar ke da matukar riba.
Yaya aka yi ka fara wannan sana’a ta wakilcin banki?
Da ina aiki da wani kamfani ne, amma kasancewar aikin akwai wahala da cin lokaci, sai na ajiye aiki na fara wannan sana’ar ta hada-hadar kudade, inda nake zaman ogan kaina kuma ina da lokacin da zan yi wasu abubuwan.
Bayan kasancewar kana samun lokacin yin wasu abubuwa, wadanne abubuwa ne kuma suka ja hankalinka ka zama wakilin banki?
Yanzu shekara hudu ke nan ina wannan aiki, kuma na samu budi sosai a ciki kuma na hadu da mutane.
Wane aiki kake gudanarwa na saukaka wa mutane wajen hada-hadar kudade?
Ko zuwanka shagona kawai ka ga irin hada-hadar da nake yi.
Kuma idan ka lura babu banki a nan kusa.
Mutanen nan yankin da shagona suka dogara wajen cire kudade da tura kudade.
Ka ga da wannan zan iya cewa na saukaka musu ta hanyar kawo musu banki kusa da su a saukake.
Yaya za ka kwatanta wannan sana’a taka ta POS wajen yadda mutane suka karbe ta da ribar da ake samu?
Karbuwarta na da alaka da yanayin mutane da yardarmu da kasamu domin yana da matukar muhimmanci mutanen su kasance sun aminta da ni a matsayin wakilin banki na kusa.
Don haka ka ga dole ya zama ina da tsabar kudi a kasa, kuma ya kasance akwai yanar gizon sadarwa mai kyau.
A wannan bangaren, nib a ni da matsala domin ina aiki da POS din FCMB ne, kuma bankin ba shi da matsalar yanar gizo, kuma ba shi da wahalar mu’amala.
Saboda yadda POS dina babu matsalar yanar gizo ya sa mutane suke son zuwa wajen cirewa ko tura kudi.
Idan kwastoma suka shagona suka na rufe watakila na je ciro kudi a banki, sai ka ga ransu y abaci, amma kuma haka za su zauna su jirani saboda sun aminta da ni.
Wannan ya sa ba na wasa wajen ajiye kudi a shago.
Maganar riba kuma ba a cewa komai. A da injin na irin sabbin kamfanonin fasahar zamanin nan ne, amma sai na lura sune cire min kudi da yawa.
Da na kwatanta da irin kudaden da ake cirewa a wasu, sai na canja na kuma tsarin banki a saukake wato Easy Banking.
Tun lokacin na samu habakar riba, kuma na samu Karin kwastomomi.
Wadannen nasarori ka samu zuwa yanzu?
Na samu nasarori da dama ta hanyar wannan sana’a ta POS. Kwanan na gyara shagona na yi fenti da sauran gyare-gyare da ribar da nake samu. Na kuma sanya talabijin a ciki domin jin dadin abokan hukda. Sannan na dauki mutum biyu aiki, ka g anima na rage wa gwamnati aiki. Yanzu ina da burin fadada harkar ta hanyar bude wasu shagonan a cikin sababbin shagunan da ake ginawa a kusa da mu. Idan na samu shago daya, zan fadada harkar in kuma kara daukar mutane aiki.
Za a iya cewa wannan sana’a da kake yi ya iganta rayuwarka?
Sosai ma kuwa. Kafin ina fara wannan harkar, ina samun tsakanin N50,000 ne zuwa N70,000 ne a wata. Amma mafi karanci ribar da nake samu a wata shi ne N100,000. Ribar na da alaka ne da yanayin hada-hadar da ya gudana da kuma yanayin yawan kudaden da ake cirewa duk hada-hada da aka yi sannan yanzu an samu masu harkar da yawa.
Sannan watakila rage kudin da ake cirewa idan an cire ko tura kudi zai kara jawo mata kwastomomi. Don haka dole ya kirkiri hanyoyin da zai jawo hankalin kwastomomi domin idan kwastomomi suka karu, riba zai karu, amma lallai da a ce da irin POS din da sauran suke amfani nake amfani, da ba zan samu ribar da nake samu ba yanzu.
Haka wannan sana’a ta canja min rayuwa matuka. Abubuwan da nake amfani da su ko a gida ne yanzu sun canja. Lokacin da na bar wancan aikin da nake yi, iyalina sun sha za mu shiga wahalar rayuwa, amma yanzu abubuwa sai suka kara kyau muka kara samun walwala da jin dadi. Ina da mata da yara uku, kuma biyu a cikinsu suna makaranta kuma duk a cikin wannan sana’a nake daukar dawainiyarsu.
Kana ganin yana da muhimmanci mutum ya samu asusun banki da katin ATM?
Ya kamata kowa ya kasance yana da asusun banki yanzu. Yanzu lokaci ya canja, yanzu kusan yin komai na bukatar asusun banki ko kuma mutum ya rasa abubuwa masu yawa. Mutane da dama suna zuwa shagona su ce in ba su asusun ajiyana za a tura musu kudi. Idan irin mutanen nan sun zo nakan ce musu su kawo katinsu na dan kasa da fasfo, kuma nan da nan sai in bude musu asusun banki a turo musu kudinsu kai-tsaye.
Da asusun ajiyarsu za su neman kananan basussuka musamman ga wadanda suka kananan kasuwanci. Lallai mallakar asusun banki a wannan lokaci da muke ciki yana da matukar muhimmanci.
An ce ko ba ka kudi, ba ka matsala, a wani zance da kuke yi cewa “babu kud, babu matsala”, haka abin yake?
Da gaske ne. Idan kana hulda da bankin FCMB, idan ba ka da kudi, za ka iya neman bashi matukar kana da asusun ajiya da su, to za ka iya karban bashin kudi. Kuma za su ba ka dama ka fara kasuwanci.
Wadannen kalubale kake ganin mutanen yankin da kake na fuskanta na hada-hadar kudade?
Gaskiya zan iya cewa rashin aikin yi ne, kuma ba wai rashin guraban ayyukan neman kudi ba ne kawai, sai dai da yawa ba su da zabi. Abin wani zai iya, watakila wani ba zai iya ba. Wannan ya sa nake shawartar matasan da suka shiga harkokin kasuwancin da sana’a. Ya kamata su yaki rashin aikin yi ta hanyar bude wa kansu hanyoyi domin akalla su samu ’yancin kansu da lokacinsu.
Me za ka fada wa mutane kan tsarin Easy Network da kuke yi?
Easy network tsari ne da yake saukaka mana lamura kuma yana da aminci sosai. Zan iya cewa ma shi ne bangare mafi muhimmanci a wannan sana’ar tamu. A wannan tsarin na Easy Network, da wahala kwastoma ya samu matsala wajen cirewa ko tura kudi. Ko da kuwa ya nuna an samu matsala, kudi zai shiga asusuna ne. da zarar an samu hakan, naka duba asusun bankina, kuma z aka kudin sun shiga.
Wace shawara za ka abokan sana’arka?
Wadanda ba sa cikin tsarin Easy Network ina ga saboda rashin sanin alfanunsa, to ya kamata su yi gaggawar shiga tsarin domin habaka sana’arsu. Da farko aka kawo min bayanin tsarin ba karbe shi ba sosai, amma da na fara amfani da shi, na kwatanta shi da sauran injunan PoS, sai nay a fi sauran riba, kuma ya fi aminci da samar da natsuwa.