Sanarwar da kungiyar tseren mota ta McLaren ta ranar 24 ga Agusta cewa sun amince su dakatar da kwantaraginsu da direbansu dan kasar Australiya, Daniel Ricciardo, shi ne sauyi na baya-bayan nan a Gasar Formula One ta 2023 mai zuwa.
Sauya shekar Fernando Alonso, wanda ya rike kambun Gasar Formula One ta Duniya sau biyu, zuwa Aston Martin, kan yarjejeniyar dogon lokaci, shi ne mafi girman matakin da aka dauka gabanin kakar Formula One ta 2023 —Kodayake wasu na ganin sauya shekar tasa ba ta kai tafiyar Ricciardo girma ba.
A baya an yi ta rade-radin cewa Oscar Piastri zai koma kungiyar Alpine har sun rattaba hannun kan yarjejeniyar daukar sa, kafin daga baya ya fito ya musanta tafiyarsa kungiyar;
Ita kuma kungiyar Williams ta rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru da dama da Alex Albon a matsayin direbanta.
Ganin wadannan sauye-sauyen, yaya jerin direbobi da za su fafata a Gasar F1 na 2023 zai kasance?
Wadanne wurare ne har yanzu ba a yanke shawarar ba? Ga abin da muka sani tabbas.
Jerin Sunayen Direbobin Gasr F1 ta 2023
Max Verstappen, Charles Leclerc, Lewis Hamilton
A kakar F1 ta 2013, fitattun direbobi; Max Verstappen, Charles Leclerc da Lewis Hamilton za su ci gaba da kasancewa tare da kungiyoyinsu.
Sergio Perez, zai kasance tare da gwarzon tseren mota na duniya, Max Verstappen a Red Bull.
George Russell zai kasance tare da Hamilton wanda ya lashe gasar sau bakwai a Mercedes
Shi kuma Carlos Sainz zai ci gaba da kasancewa abokin Leclerc a Ferrari.
A karshen kakar Formula One ta 2021 mai cike da rudani, Hamilton ya yi tunanin yin ritaya, amma yanzu ya nuna cewa zai iya amincewa da sabon kwantaragi da kungiyarsa ta Mercedes.
Wane direba ne za a iya canzawa a 2023?
Har yanzu da sauran tuna a kaba a Gasar Formula One ta 2012, domin akwai tambayoyin da ke bukatar amsa — musamman a Alpine.
Kungiyar ta yi imanin sun sanya hannu kan Piastri, amma kuma ana danganta shi da McLaren wadanda a baya-bayan nan suka raba gari da Ricciardo.
Logan Sargeant, tauraron direban Kwalejin Direbobi ta Williams, na iya maye gurbin Nicholas Latifi, wanda zai bar kungiyar a karshen shekara bayan ya shafe shekara biyu yana mata wasa, tun shekarar 2020 — kodayake ana tunanin Nyck de Vrie ya fi Logan Sargeant damar maye gurbin na Nicholas.
Akwai yiwuwar a binciki matsayin Mick Schumacher a Haas kuma ana tunanin Zhou Guanyu ko Theo Pourchaire na iya zama zabin Alfa Romeo.