✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Tsaro: Dole mu faɗakar da mutane yadda za su kare kansu – ACF

Ƙungiyar ta ce dole ne a ɗauki matakan da suka dace domin kawo ƙarshen ayyukan 'yan ta'addan a yankin.

Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta yi kira kan yadda za a faɗakar da mutanen Arewacin Najeriya, game da muhimmancin kare kansu, ganin yadda matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a yankin.

Da yake jawabi a taron kwamitin zartarwa na ƙasa na ƙungiyar, shugaban ACF, Mamman Mike Osuman (SAN), ya koka kan yadda hare-hare, satar mutane, da kisan-gilla suka zama ruwan dare a yankin.

Ya buƙaci shugabanni, masu ruwa da tsaki, da al’umma su haɗa kai wajen magance matsalolin.

“Arewa tana fama da barazanar ’yan bindiga, ’yan ta’adda, da masu satar mutane,” in ji Osuman.

“Dole ne mu ilimantar da mutane kan muhimmancin kare kansu kuma mu samar da dabaru don yaƙar waɗannan matsaloli.”

Ya yi gargaɗin cewa matsalar tsaro ba ta tsaya a iya Arewa kawai ba, matsala ce ta ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar ɗaukar mataki cikin gaggawa.

“Gwamnoni, ’yan majalisa, da sarakunan gargajiya dole su yi aiki tare don magance waɗannan matsaloli,” in ji shi.

Shugaban ya kuma yaba wa ƙungiyar League of Northern Democrats, ƙarƙashin jagorancin Dokta Umar Ardo da wasu manyan shugabannin Arewa, wanda ya ce manufofinsu sun yi daidai da na ACF.

Sai dai ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a mayar da hankali kan ɗaukar matakan gaggawa maimakon jiran mafita ta siyasa.

“Dole ne mu mayar da hankali kan bunƙasa tattalin arziƙi, ilimi, gine-gine, da tabbatar da tsaro domin sake gina Arewa,” in ji Osuman.