✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za ku yi rajistar neman aikin sojan kasa a Najeriya

Masu sha'awar neman aikin na iya shiga shafinmu daga yau Litinin.

Rundunar sojan kasa ta Najeriya ta sanar da bude shafinta na yanar gizo ga masu sha’awar shiga aikin a matakin kurtu.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce masu sha’awar shiga aikin sojin za su iya aika wa da bukatar hakan a shafi da ta bude daga yau Litinin, 15 ga watan Fabrairun 2021.

A cewarta, za a iya shigar da bukatar neman aikin a wannan shafin a wallafar da rundunar ta yi kamar haka:https://recruitment.army.mil.ng

Sharudan daukar aikin:

Rundunar ta ce dole ne duk mai sha’awar samun aikin ya kasance mutumin da aka haifa a Najeriya kuma wanda ya mallaki katin shaidar dan kasa na NIN

Dole ne mutumin da ya tsarkaka daga aikata wani laifi wanda babu wata kotu da ta taba samunsa da aikata wani laifi.

Dukkan masu neman aikin su kasance sun yi nasarar a darussa hudu ciki har da cin jarrabawar Turanci wato sun samu passes a cikin kasa da zama uku na zana daya daga cikin jarrabawar kammala karatun sakandire da aka tanadar a kasar na WAEC/GCE/NECO/NABTEB.

Dole masu sha’awar shiga aikin da shaidar kammala karatun sakandire su kasance ’yan shekara 18 zuwa sama sannan masu kwarewar sana’o’in hannu su kasance ’yan tsakanin shekara 22 zuwa 26 daya yanzu zuwa ranar 31 ga watan Mayun 2021, lokacin da za fara horar da su.

Haka kuma, dole ne maza da ke son shiga aikin su kasance tsawonsu bai gaza mita 1.68 yayin da kuma mata ake bukatar kada tsawonsu ya gaza mita 1.62 ba.