✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ku san mayukan da suka dace da fatarku

Mata da dama na son lura da fatarsu domin kawata kwalliyarsu da kuma adonsu. Ko da mace ta tara shekaru za a ga ta dage…

 Wani nau’in man fataMata da dama na son lura da fatarsu domin kawata kwalliyarsu da kuma adonsu. Ko da mace ta tara shekaru za a ga ta dage wajen kula da fatarta domin kada tsufarta ta bayyana. A kodayaushe mace ba ta so a ce ta tsufa. Babbar hanya mafi sauki da za ku kula da fatarku ita ce, ta wajen amfani da man da ya dace da fatarku.
Man Moisturizer; mai ne da ke dauke da sinadarai masu gyaran fata kuma yana kula da ruwan da ke cikin fata. Man na taimakawa wajen kare fuska daga kunar rana (sun screen). Idan za a sayi mayuka sai a rika karanta bayanin da ke jikin man, don a gane ko man na dauke da sinadarin da ke hana kunar rana (sun screen) kuma ya kasance man moisturizer ne. Bambancin mai cream da lotion shi ne, ana amfani da man cream a fuska, man lotion kuma a jiki.
·         Ku shafa man moisturizer a fuska kafin yin kwalliya.
·         Kada sunan kamfanin mai ya rude ku, domin akwai wadanda mai ya fi ruwa yawa a cikin man shafawa. Idan fatarku mai yawan gumi ce, to bai kamata ku yi amfani da wanda mai ya fi ruwa yawa a ciki ba.
·         Idan fatarku mai gautsi ce, sai ku yi amfani da man moisturizer wanda ke dauke da sinadarin mai domin samun fata mai yalki da laushi.
·         Ku sayi man da sinadaransu ba masu illata fata ba ne.
·         Kuma ku sayi wanda ba shi da kamshi sosai, saboda mayuka masu kamshi na janyo kurajen fata.