Rundunar Sojan Kasa ta Najeriya ta sanar da bude shafinta ga masu neman gurbin shiga aikin soja na 2020 a hafsoshi wato Direct Short Service da kuma Short Service Combatant.
Sanarwa da ta fitar ta Twitter ta ce rajistar kyauta ce kuma tuni aka fara ta; Duk dan asalin Najeriya mai sha’war aikin na da damar neman gurbin ko da farar hula ne shi ko mai kayan sarki.
Su waye suka cancanta su nema?
Dole mai sha’awar shiga aikin ya cika wadannan sharuddan:
- Ya kasance dan asalin Najeriya wanda aka haifa a cikinta.
- Tsawonsa ya kai mita 1.68 ga maza, 1.65 ga mata
- Ya kasance mai cikakkiyar lafiya.
- Ya kasance wata kotu ba ta taba kama shi da laifi ba.
- Ya kasance mai shekaru 23 zuwa 27 zuwa watan Jinairun 2021.
- Ya mallaki takardar shaidar haihuwa ta ainihi wacce Hukumar Kidaya ta Kasa, asibiti ko karamar hukuma suka amince da ita ko kuma takardar bayyana shekaru.
- Akalla ya kammala karatun digirinsa na farko da akalla karamar shaida mai daraja ta biyu, ko babbar difloma da akalla shaidar karamar daraja a bangaren fasaha, kimiyya ko ilimin zamantakewa daga wata makarantar da aka amince da ita.
- Ya kammala yi wa kasa hidima tare da karbar shaidar kammalawa ko kuma takardar cire shi daga ciki ga wadanda shekarunsa suka haura.
- Ya mallaki takardar shaida daga makarantar da ya kammala karatu.
- Kada ya kasance mai dauke da zane ko kowane irin nau’in rubutu a jikinsa kuma ba ya cikin kowace irin kungiyar matsafa ko ta asiri.
Ta yaya za ku iya neman aikin?
- Masu sha’awar shiga aikin za su ziyarci shafin recruitment.army.mil.ng ko kuma shafin rundunar.
- Sai ka zabi kwas din da kake da sha’awar nema.
- Daga nan za a bukaci ka dora takardun da suka hada da karamin hotonka, takardun karatu, da na shaidar haihuwa ko bayyana shekaru, takardar da ke nuna jiharka ta asali, da kuma shaidar kasancewa dan wata kungiya da ke da alaka da karatunsa.
- Sai ka fitar da takardar shaidar kammala wadannan matakai da za a turo maka nan take.
- Ana bukatar wata kotu a Najeriya ta saka hannu a shafin farko na takardar da ka fitar, sai kuma shugaba ko sakataren karamar hukuma ko wani jami’in soja da ya kai mukamin Laftanar Kanar ko sama da hakan wanda ka fito daga jiha daya da shi ya sa hannu a shafi na biyu.
- Dole ne ga duk mai sha’awar shiga aikin ya yi kokarin kammala neman daga nan zuwa ranar 29 ga watan Satumbar 2020.
Mu na yi muku fatan alheri!