✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za ku kula da fatarku

Hanyoyin da za ku iya bi don kula da fatarku

Ko wanne dan-Adam yana so ya ga fatarsa ta yi kyau kuma ya ga babu wani tabo a kanta.

Salon rayuwa mai tsafta na iya taimaka wa jiki ya kawar da matsalolin fata iri-iri.

Ga hanyoyin da za ku iya bi don kula da fatarku:

  1. Duba fata a-kai-a-kai don gano raunuka ko kuraje, saboda pimples da raunuka wani lokacin suna bayyana a kan fata ba tare da mun sani ba, kuma mutanen da suka haura shekaru 50 suna fuskantar hadarin kamuwa da cutar melanoma, cutar sankara fata mafi muni.

Ko yaya, idan aka gano shi da wuri, ciwon daji na fata yana da magani.

  1. Duk lokacin da aka yi wanka a yi kokarin shafa mai a jiki; shafa mai zai sanya fata ta zama mai haske da kyau. Man jiki yana aiki ta hanyar rike ruwa a cikin fata.

Don samun sakamako mafi kyau, a yi amfani da man shafawa a fuska da jiki da zarar an yi wanka ko aski.

  1. Shan sigari yana sa fata ta tsufa, ta zama mara haske kuma tana yamutsewa. Shan sigari yana takaita tsukewar jijiyoyin jini a cikin fata, wanda ke rage zubar jini kuma yana sa fata ta yi laushi. Wannan kuma yana lalata kofofin shiga da abubuwan gina jiki wadanda ke da muhimmanci ga lafiyar fata. Shan sigari yana kuma lalata sinadarin collagen da jijiyoyin elastin wadanda ke sa fata karfi da taushi.

Bugu da kari, yawan shan sigari na kawo cututtukan fata da busasshen lebe. Ga duk mai shan sigari, hanya mafi kyau don kare fata ita ce dainawa.

  1. Gajiya idan ta yi yawa tana haifar da fashewar kuraje da sauran matsalolin fata. Don inganta lafiyar fata – da kwanciyar hankali – a dauki matakai don magance damuwa. Samun isasshen barci, ba da fifiko ga abubuwa masu muhimmanci, rage yawan aikin da kuke yi sannan kebe lokaci don yin abubuwan da kuke jin dadi suna sa fata ta yi kyau.
  2. Cin abinci mai kyau zai iya taimaka muku ku samu fata mai kyau kuma ku ji dadin jikinku. Ku rika cin ’ya’yan itatuwa da yawa, kayan marmari, hatsin da ba a surfa ba. Amma wasu masu bincike sun ba da shawarar cewa cin abinci mai wadataccen man kifi da karancin kitse na sa fata ta yi kyau kuma ta yi haske. Shan ruwa mai yawa yana taimaka wa fata.
  3. Yawan shafa fuska da matse pimples na iya haifar da karin lalacewar fata. Matse pimples na iya haifar da tabo ko mele.