✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ku fitar da Zakatul Fitr

Bayanin yadda ake fitar da Zakatul Fitr, wadda a Hausa ake kira Zakkar Kono.

A yayin da watan Ramadan din bana ke bankwana, addinni Musulunci ya wajabta fitar da Zakatul Fitr, wato Zakkar kono da Hausa, ga kowane Musulmi.

Malamai sun bayyana cewa fitar da ita wajibi ne a duk karshen watan Ramadan ga duk Musulmin da ke da hali, namji ne ko mace.

Sahabin Manzon Allah (SAW), Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Manzon Allah (SAW) wajbata fitar da Zakatul Fitr domin kankare kurakurai da yasassun maganganun da mai azumi ya yi, sannan sadaka ce ga miskinai.”

Malamai sunbayyana cewa hikimar bayar da ita ita ce sanya wa miskinai farin ciki ta hanyar samar musu da abun da za su ci a lokacin Karamar Sallah.

Yadda ake fitarwa

Yadda ake fitar da ita shi ne, mutum zai fitar wa kansa da kuma wadanda yake ciyarwa kamar mata da ’ya’ya da iyaye  da ma’aikata da sauransu — idan sun kasance Musulmi.

“Manzon Allah Ya wajabta fitar da Zakatul Fitr ga babba da yaro, ’yantacce da bawa, daga cikin wadanda kuke ciyarwa,” kamar yadda Abdullahi bn Umar ya ruwaito.

Mai fitar da zakkar zai fara ne da fitar wa kansa, sannan sauran mutanen gwargwadon wajibcin ciyar da su a kansa.

Adadin da ake fitarwa

Kowanne mutum daya za a fitar mishi da Sa’i daya, wato Mudun Nabi hudu.

Idan babu Sa’i ko Mudun Nabin awo, ana iya aunawa da tafin hannu.

Malamai sun bayyana cewa Mudun Nabi daya daidai yake da cikin tafin hannu biyu na matsakaicin mutum.

Da me ake fitarwa?

Ana fitar da zakkar kono ce daga nau’in danyen abincin mutanen garin.

Haka kuma ana fitar da ita ne daga abin da ya karu a kan abincin rana da yinin mai fitarwa da iyalansa a lokacin.

Yushe ake fitarwa?

Malamai sun bayyana cewa ya halalta a fitar da zakkar tun daga ranar 28 ga watan Ramadan.

An kuma ruwaito cewa Sahabin Manzon Allah (SAW), “Abdllahi bn Abbas yakan ba da ita da kwana daya ko kwana biyu kafin ranar idin Karamar Sallah.”

Amma tana zama wajibi ne daga safiyar ranar Karamar Sallah, kuma ana gamawa ne kafin Sallar Idi.

“Wanda ya bayar kafin Sallar Idi tasa zakka ce karbabbiya, wanda kuma ya bayar bayan an yi Sallar Ido to wannan sadaka ya bayar kamar sauran sadakoki,” kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya bayyana.

Malamai sun ce haramun ne a jinkirta fitar da ita wannan zakka ba tare da uzuri ba.

Su wa ake bai wa ita?

Hadisi ya nuna miskinai ake bai wa Zakatul Fitr.

Wasu malamai na ganin ana iya ba da ita ga sauran mutanen da ake ba wa zakkar farilla.

Su ne: bayi, matafiya, masu bashi a kansu, masu aikin karbar zakka, masu aikin fisabilillahi, wadanda ake kwadayin su musulunta.

Wanda aka ba wa zakkar shi ma zai fitar, idan har an samu ragowa a kan abincin iyalansa.

 

An fara wallafawa ranar 10 ga Mayu, 2021.