✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za ku duba sakamakon jarabawar NECO 2020 cikin sauki

Hukumar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantar sakandare na 2020 a ranar Laraba 13 ga Janairu, 2021. NECO ta…

Hukumar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantar sakandare na 2020 a ranar Laraba 13 ga Janairu, 2021.

NECO ta ce a sakamakon jarbaawar ta SSCE an samu karin kashi 2% na daliban da suka samu akalla ‘credit’ biyar, da suka hada da darussan Lissafi da Harshen Turnaci.

Ga matakan da za ku bi domin duba sakamakon jarabawarku cikin sauki:

  • Ziyarci shafin duba sakamakon jarbawar NECO, wato https://www.neco.gov.ng
  • Zabi shekarar da ka rubuta jarabawar. Misali, 2020.
  • Zabi irin jarabawar da ka rubuta. Misali, SSCE INTERNAL (JUN/JUL).
  • Sanya lambar sirrin da aka ba ka a wurin da bayar.
  • Cike lambar rajistarka ta jarabawar a wurin da ya dace.
  • Daga nan sai sai ka latsa maballin ‘check result’.
  • Bayan haka sakamakon jarabawarka zai bayyana.

Wadannan su ne matakan duba sakamakon jarabawar NECO a saukake.

Muna addu’ar Allah Ya sa a dace.