Hukumar Shirya Jarabawa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala makarantar sakandare na 2020 a ranar Laraba 13 ga Janairu, 2021.
NECO ta ce a sakamakon jarbaawar ta SSCE an samu karin kashi 2% na daliban da suka samu akalla ‘credit’ biyar, da suka hada da darussan Lissafi da Harshen Turnaci.
- Tashar Buhari: Da N30 sai a kai ka har gida a Kano
- Makwabcina ya yi wa ’yata cikin shege
- Bayan shekaru 4 yana gwauranci, Dimeji Bankole zai auri diyar gwamnan Kebbi Bagudu
Ga matakan da za ku bi domin duba sakamakon jarabawarku cikin sauki:
- Ziyarci shafin duba sakamakon jarbawar NECO, wato https://www.neco.gov.ng
- Zabi shekarar da ka rubuta jarabawar. Misali, 2020.
- Zabi irin jarabawar da ka rubuta. Misali, SSCE INTERNAL (JUN/JUL).
- Sanya lambar sirrin da aka ba ka a wurin da bayar.
- Cike lambar rajistarka ta jarabawar a wurin da ya dace.
- Daga nan sai sai ka latsa maballin ‘check result’.
- Bayan haka sakamakon jarabawarka zai bayyana.
Wadannan su ne matakan duba sakamakon jarabawar NECO a saukake.
Muna addu’ar Allah Ya sa a dace.