✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda za ki zama cikin matan da mazan yanzu ke so’

Hajiya A’isha Babangida wata matshiya ce wadda karatunta na boko da kuma aikin da take yi ba su hana ta rungumi sana’a ba—sana’ar sarrafa kayan…

Hajiya A’isha Babangida wata matshiya ce wadda karatunta na boko da kuma aikin da take yi ba su hana ta rungumi sana’a ba—sana’ar sarrafa kayan abinci. A ganinta mazan yanzu ba sa son ba-ni-ba-ni, don haka wajibi ne mata su sauya taku, kamar yadda ta shaida wa jaridar Aminiya.

Tarihina

Sunana A’isha Babangida, ’yar asalin Jihar Kaduna; amma an haife ni a Birnin Tarayya, Abuja. Kuma a nan na girma har na yi wayo.

Na yi makarantar firamare ta Stella Marris Nursery and Primary School da ke Abuja.

Da na gama cikin nasara, sai iyayena suka yi tunanin su tura ni gida domin in yi ilimin sakandare a can; don in samu damar sanin wasu al’adunmu da sauransu.

To shi ne aka kai ni makarantar Gray’s International College da ke Kaduna. Da na gama, sai na fara karatu a Jami’ar American University of Nigeria da ke Jihar Adamawa, inda na samu digiri na farko a  Tsare-tsaren Hanyoyin Sadarwa (Communications and Multimedia Designs).

Burina ina karama

Lokacin da nake karama, kullum idan na zauna ina kallon talabijin burina shi ne in zama mai watsa shirye-shirye da karanta labaran talabijin, abin yana ba ni sha’awa sosai.

Aka zo kuma na samu na karanta abin da ya shafi haka a jami’a; amma ba wannan aikin nake yi ba yanzu, saboda yanayin rayuwa da kuma kaddara ta Ubangiji.

Kalubalen rayuwa

Rayuwa yanzu tana tare da wahala da yawa saboda za ka ga wani lokaci abubuwa ba su tafiya maka daidai yadda kake tunani.

Amma Allah kuma Shi ne Masani shi ya sa wani lokaci idan ina cikin matsala sai in tuna da Allah in ce haka Allah Ya so kuma Allah Shi ne Mai maganin komai.

Dalilina na kafa Aysha’s Halal Kitchen Spices

Ban da aikin gwamanti da nake yi na zauna na yi tunani idan mutum ya tsaya har sai an biya albashi wani lokaci ba ya kai mutum karshen wata. Sai na yi tunanin in fara sana’a ko kasuwanci; amma ba kowace sana’a ba dole in duba abin da na fi so da kuma abin da na fi kwarewa da kuma yadda zai taimaka wa al’umma.

Wannan ne sanadin fara kasuwancin da nake yi na masana’antar hada kayayyakin abinci mai suna Aysha Halal Kitchen Spices.

Abin da nake son a tuna ni da shi

Ina son kowace mace ta tuna da ni da spices ko kayan yajina, yadda ba za ta manta da Maggi ba a girkinta wannan kadai shi ne babbar nasara a gare ni.

Shawarar mahaifiyata da ba zan manta da ita ba

Kullum tana yawan tunatar da ni a kan cewa kada in ce ba zan iya yin abu ba. In rika gwadawa har sai na kware sosai.

Kuma in yawaita taimakon mutane shi ne tambarin da zan bari a duniya da Lahira.

Duk wani abin taimako in yi kokarin yin shi.

Tufa, turare, jaka da takalmin da na fi so

Gaskiya ba ni da wani abin da nafi so. Duk abin da na samu kuma ya yi mini kyau shi nake sakawa.

Yadda nake hutu

Anya ina da hutu kuwa? Saboda a kullum akwai abin da nake yi; ko dai ina cikin karatu ko aiki ko gwajin spices dina.

Amma idan na gaji nakan yi dan kallon talabijin sai in kwanta in yi barci.

Kasashen da na ziyarta

Na taba zuwa Saudiyya da kuma Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Yadda na haxu da mijina

Na fara haduwa da mijina a gidan rasuwa. Allah Ya jikan Musulmin da suka riga mu gidan gaskiya.

Daga nan kuma sai ya zo gidanmu; wannan ita ce haduwarmu ta gaba.

Ya gaishe da mahaifiyata kuma ta amince da shi, shi ke nan sai aka fara maganar aure.

Abin da na fi so daga mijina

Yana da riko da addini, gaskiya. Ba ya wasa da addininsa kuma yana da fahimta, sa’annan duk abin da na ce ina so in yi, bai taba hana ni ba, idan har ba zai saba wa addininmu ba.

Saboda haka shi ne karfin gwiwata a duk abin da nake yi a rayuwata.

Iyalina

Mun taso mu hudu da mahaifiyarmu ta haifa. Ni ce ta farko, ina da kanne uku—biyu mata sai namiji daya.

Amma ba ni da ’ya’ya tukunna.

Mawaqan da na fi so

Ban cika jin waka ba gaskiya, don haka babu wani mawaki da na fi so.

Abincin da na fi so

Ina son kaza sosai da sosai. Gasasshiya ce ko soyayyar kaza; idan har kaza ce, to zan ci.

Qungiyoyin da nake ciki

Ina da wata qungiya mai suna We Arewa Women da na fara ta taimakon matan Arewa da jin matsalolinsu.

Sa’annan ina cikin wata kungiya mai suna Open Dairies Foundation da kuma Women Council.

Shawarata ga mata

Shawarata ga mata ita ce a rike sana’a.

Duk kankantar sana’a ki yi ba ya taba rage miki komai.

Saboda mazan yanzu babu mai son macemai yawan ba-ni-ba-ni; don haka, ’yan uwana mata ina kara kira gare

ku da ku yi riko da sana’a, sa’annan ku yi karatu sosai saboda akwai matukar alfanu a ciki.

 

Mata na iya hada karatu da Aure?

Sosai ma mata na iya hada karatu da aure.