✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki yi hadin da zai kara wa gashinki tsawo

Mun san mata da dama suna da burin mallakar gashi mai tsawo da sheki da kuma laushi irin na ‘yan matan Indiya, kasancewar gashi na…

Mun san mata da dama suna da burin mallakar gashi mai tsawo da sheki da kuma laushi irin na ‘yan matan Indiya, kasancewar gashi na daya daga cikin abubuwan da ke kara wa mata kima, kyawu da kuma martaba a wurin jama’a. Idan ta wannan ne sai mu ce abu ne mai sauki, abin da ake so shi ne, ya kamata ki rika kula da gashinki sosai.
Wannan hadin da za mu yi bayaninsa a gaba zai dada sanya gashinki ya kara tsawo da laushi da kuma sheki, zai kuma hana gashinki karyewa. Muna son ki san cewa wannan hadin akan yi amfani da shi ne kamar sau biyu a wata. Idan kin kasance mai amfani da wani hadi na daban ne wanda ba wannan ba, to bai kamata ki rika hada wannan salon gyaran gashi da wani na daban ba, in ba haka ba, sai ki ga kwalliyarki ba ta biya kudin sabulu ba.

Abubuwan da za a bukata:
·         Man Amla
·         Zuma
·         Ruwan dumi

Hadi:
·         Ki zuba cokalin Amla biyu a roba.
·         Sannan ki zuba rabin cokalin zuma a cikin amla din.
·         Ki sanya cokalin ruwan dumi kamar 2 zuwa 3.
·         Daga nan ki rika juya hadin har sai ya cakudu sosai.
·         Ki taje gashinki kafin ki shafa wannan hadin a fatar kai.
·         Sannan ki jira na tsawon minti 30.
·         Ki wanke kai da man wanke gashi (shampoo).