✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki magance warin jiki

Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin jama’a, musamman lokacin zafi, idan aka hada gumi ko aka yi yawo…

Warin jiki na daya daga cikin abubuwan da ke janyo tsana a tsakanin jama’a, musamman lokacin zafi, idan aka hada gumi ko aka yi yawo a rana sai warin jiki ya rika tashi. Akan samu warin jiki ne saboda yanayin gari ko an haifi mutum da shi ko kuma ta irin abincin da ake ci. Kamar masu yawan cin tafarnuwa daga sun motsa sai an ji warinta. Don haka ne a yau na kawo miki hanyoyi mafiya sauki da za ki bi don magance warin jikin.
· Turare: Yawan fesa turare na jiki ko na hammata ko na tufafi na magance warin jiki. Amma ki sani yawan amfani da turaren jiki da ko na hammata na sanya kuraje fesowa.
· Sabulu da ruwa: Hanya mafi inganci wajen magance wannan matsalar ita ce, amfani da tsaftataccen ruwa da sabulu, don yin wanka kamar sau uku a rana, kuma ki dage wajen wanke lungun da ke janyo wari kamar hammata da sauransu.
· Wankakken tufafi: Kada ki manta duk yadda mutum ya kai ga wanka idan tufafin da yake sanyawa masu datti ne, to lallai ba zai rabu da wari ba. Don haka ana son ki rika sanya tufafi mai tsabta musamman wanda ake sanyawa a ciki, kamar dan kamfai da rigar mama da sauransu.
· Amfani da sinadarin alam: Idan warin jikinki ya kasance mai tsanani ne, to sai ki rika sanya sinadarin alam a ruwan wankanki kafin ki yi wanka, hakan zai magance miki warin jiki.
· Zuma: Bayan kin yi wanka za ki zuba kamar cokali daya na zuma a ruwan dumi, sannan ki watsa a jiki, hakan na rage warin jiki.
· Shan ruwa: Domin rage warin jiki, za ki iya shan kofin ruwa daya da sassafe kafin ki ci wani abu..
· Amfani da ruwan Rose: Za ki iya diga ruwan rose water a cikin ruwa kafin ki yi wanka, hakan na rage warin jiki da kuma kara wa jikin kamshi.