✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ka yi bankwana da warin baki

Ga hanyoyin da za ku bi domin rabuwa da warin baki cikin sauki.

Yayin da warin baki ko numfashi ke kunyata ta idan kana magana tare da takura abokin maganarka so su kawar da kai; mun tattaro muku hanyoyin da za ku bi domin rabuwa da matsalar ta warin baki.

Domin samar wa mai karatu kyakkyawar fahimta, wannan makala na dauke da bayanai a kan alamomi da abubuwan da ke haifar da warin baki da kuma yadda za a mangace matsalar cikin nasara.

Abin da ke haifar da warin baki

A likitance aka sani da halitosis, wanda ya shafi fitar numfashi ko iska mai wari daga bakin mutum.

Matsalar ta halitosis kan faru lokaci zuwa lokaci, tana iya kasancewa mai munin gaske – a wasu lokutan.

Matsalar kan samo tushe ne daga baki, inda nan ne mazaunin kwayoyin halitta na bakteriya. A lokacin da ka ci wani abu, wani dan taki daga abincin kan makale a tsakani da kuma kan hakoronka.

Sai su kuma kwayoyin Bakteriyan su yi rayuwa daga wannan abincin, daga nan sai su fara sako sinadarin sulfur – mai wari da doyi.

Idan ba a goge kwayoyin bakteriyan a kai a kai, wannan ragowar abincin kan yi cirko-cirko da hakan zai bai wa bakteriyan damar rayuwa a cikin baki, wanda wannan yanayin kan sa kananan kwayoyin su sami gindin zama a kan hakoronka, har su yi dabaro.

Yayin da ba a iya kawar da wannan dabaron ba, ta hanyar goge baki da buroshi ko asuwaki akalla sau biyu rana, sai hakan ya jawo wani yanayi mai wari, wanda a karshe zai kara ta’azzara warin da zai haifar da rubewar hakorin mutum.

Dukkan wani nau’in abinci kan iya makalewa a hakora, sai dai wasu kalolin abincin kamar albasa da tafarnuwa  sun fi haifar da warin baki.

Narkar da ire-iren wadannan nau’ukan abincin na samar da sinadarin sulfur a cikin magudanar jini. Yayin da jinin ya kai ga huhu, sai hakan ya shafi numfashin mutum.

Sauran ababuwan da ke haddasa matsalar sun hada da: bushewar baki da matsalolin hakora da wasu cututtukan da ke boye a jiki da cututtukan baki da kuma wasu magungunan.

Kaurace wa cin abinci, ita ce babbar hanyar da ke haifar da warin baki. Dalilin shi ne, idan ba ka ci abinci ba, to ana samun karancin miyau a baki.

Ba wai kawai wanke dattin ragowar abincin a baki miyau ke yi ba, a’a yana taimakawa wajen narkar da abincin ta yadda zai shige ta makogoro cikin sauki.

Illar shaye-shaye ba ta tsaya ga haifar da sinadarai masu jawo warin numfashi daga baki da kuma huhun mutum ba, a’a ta kan ma sa bushewar baki, wanda kan janyo karancin miyau a baki.

Mutanen da ke rage yawan abinci nau’in carbohydrate a cimarsu, ana ganin sun fi samun matsalar ta halitosis.

Alamomin warin numfashi

Alamomin numfashi mai wari sun hada da: warin dandano ko na bakin da bushewar baki ko kuma fari-farin abu a kan harshe.

Amma kar ka damu, ga kadan daga cikin hanyoyin magance matsalar.

Hanyoyin magance warin numfashi

Tsaftar baki

Matakin farko na kawar da matsalar shi ne yawan tsaftace baki.

Kana iya yin hakan ta hanyar yin buroshin hakora da kuma harshe akalla sau biyu kowace rana da man goge baki mai dauke da sinadaran fluoride – domin kawar da dattin abincin da kuma tsatsar hakora.

Ganyen Parsley

Wannan ganye sananne ne wajen warkar da matsalar warin baki.

Kamshinsa da kuma sinadarin Chlorophyll mai karfi da yake cikinsa na da matukar tasiri wajen saka kamshi a baki.

Cin danyen parsley bayan kowane lokacin da ka ci abinci zai yaki matsalar warin baki.

Ruwa

Busasshen baki daya ne daga cikin ababuwan da ke haifar da warin baki.

Miyau na taka muhimmiyar rawa wajen sa baki ya kasance cikin tsafta a koda yaushe. Idan ya yi karanci a baki, to kwayoyin bakteriyan kan wataya.

Yayin da mutum yake sharbar barci, bakin mutum kan bushe kayau, shi ya sa numfashi yake da wari galibi da safe, bayan tashi daga barci.

Za a iya shawo kan bushewar baki ta hanyar yawan shan ruwa. Shan ruwa, amma ba mai dauke da sinadaran caffeine ko na lemon kwalba ba, a tsawon rana, kan taimaka sosai wajen samar da miyau a baki.

Shan ruwa kamar akalla kofi takwas a kullum zai taimaka wajen samar wa da jiki ruwan da yake bukata.

Ruwan abarba

Mutane da dama sun yi amannar cewa ruwan abarba shi ne babban hanyar kawar da numfashi mai wari.

Duk da cewa babu wani binciken kimiyyar da zai tabbatar da hakan, bayanai na zahiri sun tabbatar da tasirin nasa.

Shan kofi daya na ruwan abarba bayan kowane cin abinci ko kuma mutum ya tauna yankan abarbar guda daya tak, na tsawon minti daya zuwa biyu – hanya ce ta yakar numfashi mai wari.

Yana da muhimmanci kuma a kurkure baki daga sukarin da aka sha a ’ya’yan itace da kuma lemon kwalabe, bayan an sha.

Madara

Madara shi ma an san shi wajen kawar da numfashi mai wari.

Binciken masana ya nuna shan madara bayan an ci tafarnuwa ya kan kawar da matsalar “warin tafarnuwar” a numfashi.

Shan kofi daya na madara mai matsakaicin maiko ko kuma ma wanda yake cike da maikon a lokaci ko bayan cin abinci mai cike da ababuwa masu saka wari kamar tafarnuwa da albasa, hakan kan taimaka wajen tsaftace bakin mutum tare da kawar da numfashi mai wari.

Shin ka karu da wannan makalar? Za mu so jin tunaninka.