✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za ka magance hassada a zamantakewa

Abin da ke kawao hassada, matsalolinta da kuma maganinta.

A wannan mako ina son hankalinmu ya karkata ne wajen nazarin yadda halayya ta gari da kyautata wa juna a mu’amala ta yau da kullum ke iya kawo fahimtar juna da zaman lafiya a tsakanin jama’a, musammam masu bambancin kabila, addini ko ra’ayin siyasa, da sauran harkoki da zaman tare ke iya hada jama’a daga bangarori daban-daban.

Babu shakka zaman lafiya da jama’a da tausayawa da tallafawa da kauce wa duk abun da zai iya kawo sabani a tsakanin mutane, abin a yaba ne matuka, musamman a wannan lokaci da jama’a ke cikin kunci da rashin yarda da juna, saboda kura-kuran da suke zargin wasu suna yi da gangan don cimma wata manufa ta son ransu, ko danne hakkin wasu.

Rashin yarda, zargin juna, hassada, kishi, zalunci, babakere, da tauye hakkin raunana halaye ne da aka saba gani a zamantakewa ta yau da kullum, inda wasu ke kokarin fifita kansu da tilasta bukatunsu a kan na sauran mutane, a dalilin haka kuma sai a samu turjiya da nuna rashin yarda daga wani bangare.

Mummunar halayya irin ta hassada na ruguza imani da mutuncin mutum saboda kasancewarta mugun ciwon da ke nukurkusar mai yin ta a cikin zuciyarsa shi kadai.

– Hassada na nau’o’inta

A takaice, idan aka ce hassada ana nufin wani yanayi da mutum zai rika jin wani zafi, rashin kwanciyar hankali, ko bacin rai idan ya ga wani dan uwansa, makwabci, aboki ko ma dai wani na kusa da shi da Allah Ya yi wa daukaka, ko wani alheri da shi bai samu ba.

Wasu manazarta sun kasa hassada zuwa gida uku.

Akwai hassada ta jin kyashi, wadda mutum zai rika ji a zuciyarsa don me wani zai fi shi samun wani abu a rayuwa? Alal misalin kudi, mulki, baiwa ko mukami.

Akwai kuma hassadar da mutum zai ji shi ba ya son kowa ya samu wani abin alheri ko karuwa sai shi kadai.

Sai na uku wanda shi ne ya fi kowanne muni; wato mutum ya ji cewa idan dai shi ba zai samu abu ba to, gara kar kowa ma ya samu. Irinsu ne suke zama ’yan a fasa kowa ya rasa!

– Tarkon hassada

Mutane da yawa suna fadawa cikin yin hassada ba tare da sun ankara ba.

Alal misali: Yawan yin magana a kan cigaban wani ko wata, har ya kai ga ana cewa, ‘Oh… su wane an haye, sai ka ce da ba teburinmu daya ba a wajen aiki, lokacin nan kuwa kayansa ba su wuce kala biyar ba’.

Ko mutum ya rika cewa, ‘Su wane an samu shiga, ji wai yanzu shi ne kaza, sai ka ce ba tare muke cin kwakwa ba’; ko ‘Dubi daga malami ya shigo aji sai ya fara wani iya yi wai shi a dole mai kwakwalwa.’

– Yadda hassada ke farawa

Yadda mutum zai gane idan ya fara nuna hassada shi ne, idan ya ga yana yawan nuna damuwa da al’amarin wani ko wata, wanda kwata-kwata bai shafe shi ba.

Ko kuma ka rika damuwa da son sanin halin da wata ko wani yake ciki, musamman domin ka ji ya samu cibaya ko matsala.

Haka kuma idan ka ji dadi a ranka saboda ka ji mummunan labari game da wani, ko ma ka yi dariya ko shewa; idan kuma ka ji labari mai dadi game da mutum sai ka ji ranka ya baci, ka kasa yi masa fatan alheri, ka fara jin tsoron kar ya wuce ka a wani mataki na rayuwa.

Irin hakan ke sa wani lokaci har ka fara kokarin sukansa a wajen abokan arzikinsa, ko kokarin fadin miyagun maganganu ko yin batanci game da shi, musamman ma idan ba a tambaye ka labarinsa ba.

– Kadan daga illolin hassada

Hassada tana hana mai yin ta samun cigaba a rayuwarsa, kuma duk abin da ya sa gaba ba zai ga nasara bayyananniya a kai ba.

Hassada tana rage imani kuma tana taimakawa ko ta kai mutum ga aikata shirka da fita ma daga addini ba tare da mai yin ta ya sani ba.

– Maganin haddasa

Ya kamata mutum ya yi kokarin ganin ya yaki wannan mummunar halayya ko kare kansa daga gare ta.

Yadda zai yi hakan ba wani abu ne mai wuya ba, hasali ma yin hassadar ta fi wuya!

Takurawa kanmu muke yi, sai mun yi ta duk kuwa da mun san illarta da kuma girman zunubinta.

Na farko, mutum ya yi kokarin cire kansa daga duk al’amuran da ba su shafe shi ba, ya mayar da hankalinsa a kan inganta rayuwarsa.

Kiyaye kanka daga gulmace-gulmace, son iyawa ko son ba da shawara a inda ba a nemi taimakonka ba.

Mutum ya kuma rika yi wa zuciyarsa addu’ar tsarkakuwa daga dukkanin miyagun ayyukan da ka iya gurbata ta.

– Son kai shi ne tushen hassada

Wannan bakar halayya ta hassada na da nasaba da yadda mutum kan nuna son kansa fiye da maslahar sauran jama’a.

Mutane masu son kansu suna haifar da damuwa, kunci da kiyayya mai yawa, saboda sun fifita son zuciyarsu a kan amfanin da jama’a da dama za su samu.

A kan abu kalilan da wani yake kwadayin samu sai ya rusa jin dadi da kokarin da wasu suka dade yana yi.

Mun sha jin korafe-korafe daga mutanen da aka tauye wa hakki ko aka zalunta, saboda son zuciyar da wani ya nuna musu, don kawai ya samu damar da zai yi abin da ya dace amma ya kasa, saboda zarmewa da son zuciya.

Akwai mutanen da za ka rika yi musu kallon manya ana girmama su saboda matsayin da suke da shi, ko arzikin da Allah Ya ba su, har ma ka ji ana yi musu kirari, don kwadayin samun wata alfarma daga wajensu.

Amma da za ka ji abin da wadanda ke karkashinsu ko iyalinsu suke fada, ba za ka sake kallon su da martaba ba, saboda yadda suke kin fitar da hakkin masu yi musu kwadago da guminsu da kin sauke nauyin iyali da ’yan uwa da ke kansu.

Irin wadannan mutane suna ganin idan idan suka cire wani abu daga arzikinsa zai rage musu jin dadi, ko kuma tamkar za su bayar ne a inda ba a san zafinsu ba.

– Dan karamin misali

Yana yi wa mutane wahala su sadaukar da wani yanki na jin dadinsu, walwala ko damar da suke da ita don yi wani ya amfana.

Sai ka ga ana ta fama da wani a cikin motar haya kan ya dan gyara zamansa domin kowa ya ji dadin zama, amma ya yi mirsisi, saboda tunanin idan kowa ya zauna da kyau shi ba zai sake yadda yake so ba.

Haka ma ko a gaban ubangiji wajen sauke farali, za ka ga wani ya yi babakere a waje, ana rokon sa ya gyara zama ko tsayuwar cikin sahu, amma yana ganin za a takura masa, shi ba zai yarda ba.

A duk yayin da mutane suka fahimci wane yana da halin rowa, son kai da rashin sassauci a harkokin rayuwa, to yana zama abin kyama, ana kaffa-kaffa da shi.

– Mene ne abin yi?

Kyautatawa da nuna halin kwarai suna sanya kaunar mutum a zuciyar abokan zamansa da sauran ’yan uwa.

An sha samun asara mai yawa ta rai ko ta dukiya da bacin rai mai tsanani saboda wani ya kasa hakuri a samu yadda ake so, ko kuma ya yi abin da ya kamata daga bangarensa, don yana ganin ba shi ne zai amfana ba, ko kuma idan ya yi haka zai takura.

E, ba a ce lallai mutum ya rika takura wa kansa don jin dadin wasu ba, amma kyautatawa tana da amfani, kuma akwai alheri da ke bin bayan sadaukarwa ta tsakani da Allah.

Ba kowanne lokaci ne yin abin da ya kamata ke zama takura ba, wani lokaci sauke nauyi ne.

Kai ma wani lokaci za ka nemi wani abu daga wajen wani, wanda kake ganin ya kamata ya yi maka, idan bai yi ba kai ma ba za ka ji dadi ba.

Mutane masu son zuciya ba sa taba samun wadata da gamsuwa da rayuwarsu, ko da kuwa sun samu damar yin duk abin da suke so, saboda kodayaushe tunaninsu ba ya wuce jin dadin kansu ta hanyar kuntata wa wasu.

Don haka kirana ga mai karatu shi ne a guji fifita son rai, domin an ce son zuciya bacin zuciya!

Allah ya taimake mu!

Abba Abubakar Yakubu, ya rubuto wannan mukala ne daga Jos, [email protected]