Ministan lafiya na Najeriya Osagie Ehanire ya yi gargadi kan yiwuwar karuwar mace-mace sakakamon yawan wadanda ke kamuwa da cutar COVID-19 a kasar.
Osagie Ehanire ya shaida haka ne sadda yake bayyana matakan kare yawaitar mace-macen ta hanyar bai wa wadanda suka fi hadarin mutuwa daga cutar kulawa ta musamman.
“Tun da a bayyane take cewa wadanda suka fi hadarin rasuwa sakamakon cutar sune masu shekaru sama da 50 da ke fama da cututtukan da suka hadar da ciwon siga, kansa, hawan jini, ciwon koda, cutar AIDS da sauransu, za mu ba wa wannan rukuni na masu cutar COVID-19 kulawa ta musamman.
“Matakan sun hadar da takaita fitarsu waje domin kare su daga kamuwa da ita ta hanyar ba su shawarar zama a gida, ko su amfani da takunkumi a duk sadda ya zama tilas su fita, ko kuma a lokacin da suke tare da masu yawan fita waje.
- Za mu hukunta likitocin da ke yajin aiki —Minista
- Za mu kwace lasisin duk likitan da ke watsi da marasa lafiya – Minista
- Coronavirus: Ma’aikatan lafiya 29 sun kamu, an rufe asibiti a Filato
“Sannan zuwa wuraren da ke hada cunkoso, kamar kasuwanni da wuraren ibada na da hadarin yada cutar gwargwadon dadewar mutum, musamman ga rukunin da cutar tafi yi wa illa, saboda yiwuwar yaduwar cutar na da alaka da tsawon lokacin da masu ɗauke da ita suka yi a cikin taron jama’a”, inji shi.
Ministan ya kara da cewa mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar amma suka zabi su yi jinyarta a gida to su tabbatar sun ziyarci cibiyoyin kula da lafiya da zarar sun fara jin alamar zazzaɓi ko wani ciwon.
“Ba zai yiwu su yi jinya a gida ba, domin rashin lafiya ka iya cin masu cikin dare ko lokacin da ba za a iya kawo musu dauki cikin gaggawa ba. Don haka irin wannan rukuni na jama’a dole a yi jinyarsu a cibiyoyin da aka tanadar.
“Jinkiri wajen ba wa masu cutar kulawa ka iya haddasa mutuwarsu fiye da yadda ake zato, don haka idan aka kula da wadanan matakai za a iya rage yawaitar mace-mace”, inji shi.
Ya ce annobar na cikin jama’a tana kara yaduwa ta kuma kama muhimman mutane da dama, saboda haka alhaki ne a kan kowa ya ba da gudunmawa wajen dakile yaduwarta.
“‘Yan uwa da abokan arziki na da rawar takawa ta hanayar ba da shawarwari a kan matakan kariya. Ta haka ne za a yi nasara har a kawar da annobar”, inji shi.
Zuwa lokacin hada wannan rahoton mutum 18,480 suka kamu da cutar a Najeriya yayin da mutum 6307 suka warke, sai kuma mutum 475 da aka rasa a sakamakon cutar.