✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance tabo a fata

Kwanakin baya an rika turo mana sakonni ana bukatar bayani kan yadda za a magance tabo a fata musamman ma a fuska, don haka a…

Kwanakin baya an rika turo mana sakonni ana bukatar bayani kan yadda za a magance tabo a fata musamman ma a fuska, don haka a wannan makon filin Kwalliya zai yi gamsasshen bayanin yadda za a magance matsalar tabo a fuska.
Akwai hanyoyi masu yawa da ake bi wajen magance tabo a fuska, sai dai idan mun yi muku bayaninsu muna so ku yi amfani da hanya daya, idan bukata ba ta biya ba sai ku gwada daya kuma. Idan aka cakuda su, to ba za a samu biyan bukata ba.
Itacen turaren wuta da zuma
A nika itacen turaren wuta, sannan a hada da zuma, sai cakuda su. Daga nan a shafa a fuska ko wurin da yake dauke da tabo, bayan minti 30 sai a wanke da ruwan dumi. Itacen turaren wuta na tayifar da tabo sosai, kuma yana taimakawa wajen haskaka fata. Yawan shafa zuma zalla a tabo na batar da shi. Amma sai an yi hakuri domin sauki sai a hankali. Za a iya amfani da wannan hadin na tsawon wata 3 kafin a samu biyan bukata.
kwallon dabino da man kwakwa
Wannan hadin na taimakawa wajen batar da tabo musamman wanda aka samu daga kunar wuta ko ruwan zafi. A gasa kwallon dabino sai a nika shi, sannan a hada da man kwakwa. Sai a shafa hadin a wurin da yake dauke da tabo. Za a iya samun kamar kwallon dabino 10 a wannan hadin.