✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a kawo karshen Boko Haram —Tsohon mayaki

Idan gwamnati ta bi wannan hanyar, mayakan Boko Haram fiye da 2,000 za su mika wuya

A makon jiya ne jaridar Aminiya tattauna da wani tubabben dan kungiyar Boko Haram mai suna Abdulwahab Usman, dan asalin garin Bama a Jihar Borno, inda ya ce ya yi shekara biyar yana cikin qungiyar, kafin ya tuba ya mika wuya ga hukuma a watan Disambar bara. Ya ce bai bai taba tsammani zai kawo yanzu ba a kashe shi ba.

Yaya za ka bayyana zamanka a wajen gyara hali?

A lokacin zamanmu a wannan sansani mun ji dadi sosai, domin abin da ba mu yi tsammani daga Gwamnatin Najeriya ba ne muka tarar a wajen. Inda ake kula da mu sosai aka kuma koya mana sana’o’i. Ba a kashe ko daya daga cikinmu ba kuma babu tsangwama.

Wace sana’a ka koya a wajen?

Na koyi sana’ar aski a cikin sana’o’in da aka koya mana na walda da kafinta da sauransu. Kuma idan na koma garinmu zan ci gaba da yi, ba zan sake komawa harkar Boko Haram ba.

Zamanku a wannan gari na Malam Sidi, wane canjin rayuwa ka samu?

Zamanmu a garin Malam Sidi ya sauya mini rayuwa sosai, domin a lokacin da na tsinci kaina a matsayin dan Boko Haram, ban yi tsammanin zan kasance a raye har zuwa yanzu ba; har ma in yi tunanin cewa zan sake zama mai amfani a tsakanin al’umma. Saboda a kullum muna daji ana neman a kashe mu, mu ma muna neman su mu kashe su; kowa bai da kwanciyar hankali.

Kai ka shigar da kanka Boko Haram ko tilasta ka aka yi?

Ba ni na shigar da kaina Boko Haram ba. Na zama dan Boko Haram ne a lokacin da wasu abokaina da muka yi sakandare tare suka shiga kungiyar aka zo ana nemansu, saboda ba a same su ba sai aka kama ni aka tafi da ni Barikin Soji na Giwa Baracks da ke Borno.

A wani hari da ’yan Boko Haram din suka kai ne suka kama mu suka tafi da mu daji. Wannan ne sanadiyyar shigata kungiyar har na shekara biyar kafin daga bisani in mika wuya ga sojoji.

Tun shigarka kungiyar wane irin hare-hare ka taba kaiwa?

Na kai hare-hare masu yawa sannan kuma haduwa muke yi muna kai wa sojoji hari, mu kashe na kashewa wasu su gudu.

Sai dai ni a kashin kaina ban taba kashe farar hula kai tsaye ba sai hukuma kuma ban taba yunkurin kunar bakin wake ba sai dai hari da bindiga.

Ganin ka tuba yanzu, mene ne kiranka ga sauran da suke daji?

Kirana ga sauran ’yan bindigar da suke daji shi ne su mika wuya ga gwamnati kamar yadda muka yi.

Su ajiye makamai, ba za a kashe su ba domin mu ma ba a kashe mu ba; domin kasa ta zauna lafiya.

Wane tabbaci za ka bayar na cewa ba za ka sake komawa Boko Haram ba?

Tabbacin za mu zama ’yan kasa nagari ne ya sa aka ba mu Alkur’ami mai girma muka rantse a kan ba za mu sake komawa wannan kungiyar ba, duk rintsi duk wuya.

Tun da gwamnati ta yi mana abin da ba mu yi tsammani ba shi ya sa ba zan sake komawa Boko Haram ba.

Yaya za ka kwatanta rayuwarku a daji da kuma yanzu?

Zamanmu a daji a cikin hadari muke, domin kullum tunaninmu shi ne ta ina za a bullo a kashe mu. Kullum jirgi yana yawo a kanmu yana kashe mu muna gudu muna buya kuma rayuwarmu cikin wahala ce a kullum.

Sannan wani hari da muka taba kaiwa a garin Konduga, mu 76 aka kashe, mutum 33 a cikinmu kuma muka tsira da kyar. Wannan ma yana daga mini hankali sosai.

A matsayinka na tsohon dan Boko Haram ya kake ganin za a iya kawo karshen lamarin?

Idan gwamanti tana son a kawo karshen Boko Haram, sauran da suke daji su mika wuya.

Gwamnatin Najeriya ta je daji ta yasar da takarda, cewar su mika wuya ba za a kashe su ba.

Domin mu ma takardun muka gani shi ya sa muka mika wuya kuma kamar yadda mu kimanin 601 muka mika wuya, idan aka yasar da takardar suka gani fiye da mutum dubu biyu za su iya mika wuya, tunda sun ga mu ba a kashe mu ba, an mana gyaran tarbiya; mun koma ga iyalanmu.