Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta fitar da sakamakon jarabawar (UTME) da aka zana ranar 3 ga Yuni, 2021.
An gudanar da jarabawar a dukkanin cibiyoyin da aka ware na CBT a fadin kasar nan.
- Yadda Pogba ya cire kwalbar giya a gabansa
- Mun gano Ministar da ta sayi kadarar Dala miliyan 37 a boye — EFCC
Wata sanarwa da mai magana da yawun JAMB din, Dokta Fabian Benjamin, ya fitar a ranar Laraba, ta ce sakamakon mutum 62,780 ne ya fito daga cikin dalibai 160,718 da suka zauna jarabawar.
Ga matakan da za a bi don duba sakamakon jarabawar:
- Ziyarci shafin JAMB a https://jamb.gov.ng/efacility
- Shiga “UTME 2021 Mock Results Notification Slip”
- A ciki za a ga inda za a sa lambar jarabawar.
- Idan aka sa lambar a wajen aai a danna neman sakamakon jarabawa.
- Sai a jiya, bayan dakikoki sakamakon zai bayyana.
Kazalika, za a iya duba sakamakon jarabawar ta wannan hanya:
- Shiga shafin JAMB a jamb.gov.ng
- Saka adireshin email da lambobin sirrin da aka yi amfani da su yayin rajistar UTME 2021.
- Sai a danna nemo sakamako.
- Sakamakon jarabawar zai bayyana cikin PDF, sai a fitar da shi.