✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a ceto harsunan da ke barazanar bacewa

Wani bincike na Hukumar Raya Al’adu da Ilimi ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO) ya bayyana cewa a Najeriya, kashi daya cikin hudu na yara ’yan…

Wani bincike na Hukumar Raya Al’adu da Ilimi ta Majalisar dinkin Duniya (UNESCO) ya bayyana cewa a Najeriya, kashi daya cikin hudu na yara ’yan kasa da shekara 11 basa jin harshensu na asali, rahoton ya kuma yi gargadin cewa idan ba a yi wani abu ba, harsunan Najeriya da dama za su bace cikin kasa da shekaru 60 masu zuwa. A makon jiya ne Shugaban bangaren Harsuna na Ma’aikatar Ilimi, Rabaran Anota Ademola, ya ce kasar nan za ta iya asarar yaruka 152 wadanda ba a amfani da su sosai.

Ya bayyana hakan ne lokacin bikin kaddamar da wata manhaja wadda za ta dinga koyar da harsunan kasar nan, inda ya ce idan ba a dauki wani mataki ba akalla za a yi asarar yaruka 400. Ya ce harsunanmu na asali da dama ba a koyar da su a gidaje. Kodayake, ba wannan ba ne karon farko da za a ankarar da al’umma kan wannan matsalar ba.
Hukumar UNESCO ta ce Najeriya tana da yaruka 16 da suke barazanar bacewa. Akwai kuma wasu guda 10 da suka bace, ciki harda yaren Ajawa da ake amfani da shi a wani yanki da ke Jihar Bauchi, da yaren Auyokawa wanda ake yi a yankin da ake kira Jigawa a yau, da yaren Basa-Gumna wanda ake yi a yankin Kainji dukkansu sun rigaya sun bace a yanzu.
A cikin watan Fabrairun bana ne, Shugaban kungiyar Masu Nazarin Harsuna Farfesa Chinyere Ohiri-Aniche ta ce akwai akalla harsuna 400 da suke barazanar bacewa a kasar nan. Kuma ta bayyana hakan ne lokacin bikin ranar tunawa da Harshen Uwa wanda Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta shirya. Ta kara da cewa: “Babban damuwarmu shi ne yadda ba ma iya bai wa yaranmu yarukanmu a gidaje da makarantu.”
Harsuna suna mutuwa da kansu saboda kauran jama’a daga wuri zuwa wuri. Wannan na sanya su cudanya da wasu yarukan, inda akan samu auretayya. Har ila yau, zama a bariki yana kara taimakawa wajen mutuwar wasu harsunan.
A lokuta da dama iyaye da ’ya’yansu sukan rungumi harshen da ya fi tasiri a wurin da suke zaune koma-bayan nasu. Saboda yadda harshen Inglishi yake samun karbuwa da kuma muhimmancinsa wajen mu’amalar yau da kullum wannan ya sa wasu iyaye fara amfani da shi wajen yin magana da ’ya’yansu.
Wata hanya da za a iya yaki da barazanar da harsunan asali shi ne tsarin ilimi da ya bukaci koya wa yara harshensu na asali a shekara biyun farko na karatunsu. Damuwar nan ita ce ba a aiwatar da hakan musamman ma a makarantu masu zaman kansu.
Har ila yau, a wuraren da ake koyar da manyan harsunan Najeriya uku wato harshen Hausa da Yarbanci da kuma Ibo, akwai dimbin jama’a da ba a koyar da su harshensu na asali saboda manyan harsuna ukun ba sa daga cikin yarukansu na asali.
Harshe na da matukar muhimmanci wanda ya dara na amfani da shi kadai; saboda idan harshe ya bace; to fa tarihi da tsarin adabi da kuma al’adunsa duka sun bace tare da shi ke nan. Hakazalika, tushen jama’a da abubuwan da suka bambanta su da sauran.
Kodayake ba a makara ba, za a iya kai wa harsunan dauki, akalla domin karesu daga barazanar bacewa. Matakin farko dai shi ne iyaye su fara yin amfani harsunansu ga ’ya’yansu. Kuma yakamata su yi hakan da alfahari; saboda alhakin kare yarukansu daga bacewa ya rataya a kansu kamar yadda ya rataya a wuyan gwamnati. Hakazalika, gwamnatin tarayya da na jihohi. Kuma ya dace a karfafa amfani da harsunan asali a makarantu da kafafan yada labaru da kuma aiwatar shirin kayor da su a shekara biyu na farko a makaranta.
kungiyoyin al’umma za su iya ba da tasu gudunmuwar wajen samar da littattafan adabi na harsunan kasar nan domin hakan zai bai wa jama’a kwarin gwiwa da sha’awar amfani da yarukan gida.