Ƙungiyar Likitoci Masu Ba da Agaji ta Duniya da aka fi Sani da MSF a kwanakin baya ta fitar da sanarwa ta nuna damuwa a kan yawaitar yaran da ke fama da yunwa a sansanoninta da ke jihohi bakwai na Arewacin ƙasar nan.
Jihohin da abin ya shafa a cewar sanarwar da ƙungiyar ta fitar ɗauke da sa hannun Jami’in Hulɗa da Jama’arta a Nijariya Abdulkareem Yakubu sun haɗa da Kano da Bauchi da Borno daYobe da Sakwato da Zamfara da kuma Kebbi.
- Lakwaja: Birnin da manyan kogunan Nijeriya suka haɗu amma ba ruwan sha
- An ƙone jabun magunguna na N985m a Kano
Ƙungiyar mai cibiyoyi a ƙasashen duniya ta ce a sansanoninta da ke Arewacin Nijeriya ta samu ƙaruwar yaran da ke fama da yunwa wadda ke jefa rayuwansu a cikin haɗari.
Ta ce abin mamaki alƙaluma sun nuna an samu ƙarin kusan kaso ɗari.
“Mu a wajenmu wannan abin tayar da hankali ne duk da an yi hagen haka na iya faruwa ne a watan Yulin ban.
“Yanzu muna lura da majinyata a kan tabarmi saboda sansanoninmu a cike suke. Kuma yaran sai mutuwa suke yi,” in ji ƙungiyar
“Idan ba a ɗauki matakai cikin gaggawa ba, akwai yiwuwar wasu rayuka su salwanta. Dole ne kowai ya ba da gudunmawa wajen kare rayukan yara domin yara a Arewacin Nijeriya su girma cikin aminci ba tare da yunwa ba, ko kuma illolin yunwar ba,” in ji wakilin Ƙungiya MSF a Nijeriya, Simba Tirima a cikin sanarwar.
Ƙungiyar MSF ta yi kiran neman taimakon gaggawa tare da kira ga shugabannin Nijeriya da ƙungiyoyin ƙasashen duniya da suke ba da taimakon gaggawa su ɗauki matakan da suka dace wajen magance matsalar yunwa da yara ke fama da ita tare da magance tushen rikicin da ake fama da shi a Arewa.
Kano
Lokacin da Jaridar Aminiya ta ziyarci Sashen Yara na Asibitin Hasiya Bayero a Jihar Kano, ta ga yaran da suke fama da yunwa masu yawa a kwance.
Akasarin iyayen da aka zanta da su sun danganta matsalar yunwar da hauhawar kuɗin kayan abinci a ƙasar nan.
Wata mahaifiya mai ’ya’ya 12, Hauwa Adamu Bachirawa ta shaida wa Aminiya cewa da ƙyar suke cin abinci sau uku a rana ballantana ta shirya wa ‘yarta marar lafiya abinci na musamman da likitoci suke ba da shawara.
“A lokacin da na lura tana ramewa sai na ɗauke ta zuwa asibiti sai aka faɗa min cewa taba fama da yunwa,” in ji ta.
“Wata ma’aikaciyar asibitin ta shaida min cewa tana fama da cutar yunwa, saboda rashin samun abinci marar gina jiki, sai ta shawarce mu kan mu inganta abincinta. Amma kuma ba za mu iya saye ba.
“Wannan shi ne dalilin da jikinta ya tsananta. Bari in faɗa maka gaskiya da ƙyar muke cin abinci ko da marar gina jikin ne sau uku a rana,” in ji ta.
Ta kuma ce tana bai wa yarinyar ce duk abincin da aka samu. “Ka san halin da ake cikin na matsin tattalin arziki a ƙasa. Tuwo muke ci da miyar kuka sai kuma shinkafa idan an samu,” in ji ta.
Wata mata mai suna Rukayya Usaini ta shaida wa Aminiya cewa ɗanta na takwas ne ke fama da rashin lafiya.
Shugabar Sashen Kula da Abinci Mai Gina Jiki na Asibitin Hasiya Bayero a sashen yara, Hajiya Lami Idris Babale cewa ta yi sashen a ‘yan kwanakin nan ya samu ƙaruwar yaran da ke fama da matsananciyar yunwa wadda ke barazana ga rayuwarsu.
“Zan iya faɗa maka cewa a yanzu muna samun yawaitar iyayen da ke kawo yaransu fiye da a baya,” in ji Lami Babale.
Ta ƙara da cewa cutar yunwa ko tamowa a yanzu ba a karkara kurum ake samu ba, har a birane. Ta ce cutar an fi samunta ce a cikin gidaje da iyalai ke da yawa.
Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da ɗaukar matakai domin magance matsalar cutar yunwar.
Shugabar Sashen Kula da Abinci a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, Hajiya Rakiya Balarabe ta shaida wa Aminiya cewa gwamnatin jihar tare da taimakon Ƙungiyar MSF tana ƙoƙarin samar da abinci na musamman domin bai wa yaran da ke fama ta cutar tamowa ko yunwa.
Har ila yau gwamnatin na shirin farfaɗo da cibiyoyi ko sansanoninta a jihar tare da gina sababbi domin yaƙi da cutar a tsakanin yara.
Ta ƙara da cewa gwamnatin jihar na da shirye-shirye domin yaƙi da cutar yunwa ko tamowa a jihar.
“Muna da shirye-shirye don inganta rayuwar mata masu juna biyu da masu yara ’yan ƙasa da shekara biyar domin kariya daga cutar yunwa a jihar.
“Muna da shirye-shirye inda muke raba magunguna ga mata masu juna biyu da yara ƙanana,” in ji ta.
Borno
A Jihar Borno rashin damar da ’yan gudun hijira za su yi noma saboda rikicin Boko Haram ya ƙara tsananta matsalar yunwar wanda hakan ya sa cutar yunwa ta yawaita a jihar.
Bintu Komai matar aure mai ’ya’ya bakwai wadda ɗaya daga cikin ’ya’yanta ke cikin dubban yaran da ke fama da cutar yunwa a jihar a sansanin ‘yan gudun hijira cewa ta yi suna fama da yunwa tun da suka iso sansanin a Maiduguri daga garuruwansu na asali.
“Matsalar tsaro har yanzu abar damuwa ce. Shi ya sa yunwa ta zama ruwan dare a ko’ina a asibitocin jihar.
“Muna roƙon Gwamna Zulum ya haɗa kai da sojoji a buɗe garuruwa don mutane su samu damar yin kasuwanci da noma a samu abincin da za su ci gaba da rayuwa.
“Muna buƙatar damar komawa gonakinmu. Hakan ne kurum zai magance matsalar yunwar,” in ji ta.
Da suke tattaunawa da ɗaya daga cikin wakilanmu wasu daga cikin ’yan gudun hijirar da wasu mazauna gari sun ce rashin samun isasshen abinci ne babban dalilin yunwa da ake fama da ita wadda ta jefa yara masu yawa cikin mawuyacin hali musamman a cikin ’yan gudun hijira.
A cewarsu da aka tsugunar da su ɗan abin da gwamnatin jihar take ba su na taimaka musu ne na wasu ’yan lokuta. Kuma da ya ƙare suka ƙoƙarta zuwa gonakinsu sai ‘yan ta’adda su ƙwace amfanin gonar.
Sun ƙara da cewa yunƙurin fara sana’ar saro itatutuwa don yin gawayi ma ya ci tura saboda kisan gillar da ’yan ta’addar ke musu a daji.
Sun ce, “Abin da kawai muke yi shi ne sare itatutuwa don sayarwa. Ƙungiyoyin masu zaman kansu sun daina ba mu abincin wata-wata saboda gwamnatin jihar ta hana.
Hakan ya sa dole mu riƙa ɗaukar kasada wajen shiga daji domin yin itacen girki don mu sayar mu samu na abinci.
“Gwamnatin jihar ta ba mu tallafin wata uku a lokacin azumin watan Ramadan wanda ya taimaka mana. Ina faɗa maka sau ɗaya muke cin abinci a gidana ni da ’ya’yana ƙanana.
“Matsalar mu a nan ita ce abinci da ruwan sha. Hana mu shiga daji da sojoji ke yi saboda ’yan Boko Haram na hana mu zuwa yin kasuwanci tare da yin aikin ƙwadago domin ciyar da iyalanmu,” in ji wani ɗan Sabuwar Marte.
Wani ma’aikacin lafiya Bulama Abdullahi ya koka game da ƙaruwar yaran da suke fama da yunwa a sansanonin Ƙungiyar MSF a Maiduguri.
Ya ce duk da gwamnatin jihar na ƙoƙarin raba abinci da sauran tallafin ga iyalai, wanda hakan na taimakawa matuƙa, amma har yanzu akwai iyalan da ba sa iya samun abinci mai gina jiki don ciyar da ’ya’yansu.
“Gaskiya ina yaba wa ƙoƙarin Gwamna Zulum, wajen rarraba abinci ga ɗimbin mutanen da abin ya shafa a jihar.
“Sai dai abin baƙin ciki matsalarmu a Jihar Borno ta daban ce, saboda ayyukan ’yan ta’adda sun sa abubuwa sun taɓarɓare tuntuni.
“Ba na jin akwai wata jiha da ta tallafa wa iyalai kamar yadda muke yi a Jihar Borno. Haƙiƙa Gwamna Zulum yana bakin ƙoƙarinsa a wannan fanni,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa “An samu ƙaruwar cutar yunwa ta rashin abinci mai gina jiki a makonnin nan musamman a garuruwan Jere da Konduga da Marte da Maiduguri da sauran garuruwa.
“Wuraren duba marasa lafiya da ke Gwange a bayan CBN duka a cike suke da jama’a. Ya kamata a duba yadda za a taimaka wa iyalan waɗanda suke cikin wani hali.”
Lokacin da aka tuntuɓi Shugabar Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) na ofishin Jihar Borno, Misis Phuong T. Nguyen, ta ce yawaitar masu ɗauke da matsalolin ya yi munin da ya dagula lissafin rikicin Arewa maso Gabas.
Ta ce iyalai da dama na faman ƙoƙarin samar wa ’ya’yansu abin da za su ci sakamakon hauhawar farashin kayan abinci da ƙarancin wuraren noma saboda matsalar tsaro da ta addani jihohin Borno da Adamawa da Yobe.
“A lokacin bazara akan samu ƙarin yara ’yan ƙasa da shekara 5 da ake sa ran su kamu da cutar yunwa.
“Daga watan Janairu zuwa watan Maris na shekarar 2024 cutar tana da kaso 40 ne, fiye da adadin na bara.
“A watan Afrilun bara yara dubi 40 ne aka gwada su da suke fama da wannan matsala.
“Wannan cuta tana tare da barazanar mutuwar masu ɗauke da ita matuƙar ba su samu kulawar da ta dace da wuri ba.
“A halin da ake ciki Asusun UNICEF da haɗin gwiwar wasu ƙungiyoyi suna aiki tuƙuru don hana yaɗuwar cutar a tsakanin ƙananan yara a jihohin Borno da Adamawa da Yobe,” in ji ta.
Gundumar Gagi da ke Ƙaramar Hukumar Sakkwato ta Kudu a Jihar Sakkwato ita ce mai dauke da mafi yawan irin wadannan yara da ke fama da matsalar cutar yunwa ko tamowa saboda daruruwan yaran da take da su da ba su samun abinci mai gina jiki a sansanonin ’yan gudun hijira.
Yankin ya hada iyaka da wuraren da suke fama da matsalar tsaro a Ƙaramar Hukumar Raɓah a jihar.
Bincikenmu ya gano asibiti daya ne tal ke dauke da yara 20 da masu dauke da cutar.
Ɗaya daga cikin masu kula da asibitin garin Gagi, Miƙdad Ibrahim, ya danganta ruruwar lamarin da rashin tsaro da rashin samun wadataccen abinci mai gina jiki da kuma rashin yin allurar riga-kafi, sai kuma ƙuncin rayuwa da na tattalin arziki da ake fama da su a ƙasar nan.
“A kowane wata mukan raba katan 100 na sarrafaffen abinci da aka fi sani da tamowa da kuma katan 60 na abincin da ke dauke da sinadarai da ake kira SƘ-LNS, wanda wannan adadin ya kasa sosai domin matsalar ƙaruwa take yi ba raguwa ba,” in ji shi.
Ya ce, abincin tamowa na magance rashin abinci mai sinadaran gina jiki ne.
Ibrahim ya ce suna buƙatar ƙarin katan 40 a kan wanda ake ba su domin su cike giɓin da ke akwai.
Sai ya ce asibitin ya kasa matuƙa domin cikin marasa lafiya sama da 20,000 da ke zuwa asibitin a cikin wata guda, 9,000 daga ciki na zuwa ne kan batun rashin abinci mai lafiya ne.
“A daidai wannan lokaci da nake magana da kai babu sashen kula da ƙananan yara a asibitin kuma ga shi matsalar ta fi kama yara ’yan ƙasa da shekara biyar.
Ya koka game da tsananin da ake fama da shi a fadin ƙasar nan, inda ya ce wasu daga cikin daliban da ake lura da su kan matsalar a kan sake dawo da su kan wasu lalurori daban, saboda iyayensu ba su da ƙarfin samar musu da abincin da jikinsu ke buƙata.
Wani ƙwararre a fannin da ke aiki da Asusun UNICEF a Sakkwato, Abraham Mahama, ya ce yara 50,000 cikin 297,832 da ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki akan kwantar da su a asibitoci daban-daban da Asusun UNICEF ke tallafawa a jihar tun daga watan Mayun 2023.
Sakkwato ta ware kashi 15 na kasafin shekarar 2024 don yara masu cutar tamowa — Mataimakin Gwamna
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce, ta ware kaso 15 cikin 100 na kasafinta na 2024, domin yaƙi da cutar tamowa a jihar.
Mataimakin Gwamnan Jihar, Injiniya Idris Gobir ne ya bayyana haka a wajen bikin Ranar Noma ta Duniya da Ƙungiyar Medicine San Frontier (MSF) da hadin gwiwa da Ma’aikatar Lafiya ta jihar suka shirya. Jihar ta kasafta Naira biliyan 270.1 a shekarar 2024.
“Mun damu matuƙa ganin yadda matsalar take yaduwa a jihar. Gwamnatinmu ta tsaya ƙyam wajen duba lamarin da ke ci mana tuwo a ƙwarya,” in ji shi.
Gobir ya yaba wa Ƙungiyar MSF kan irin gudunmawar da take bai wa jihar wajen yaƙi da matsalar. Ya ce, jihar ta ƙaddamar da rabon magungunan tamowa a jihar.
Kwamishinar Lafiya ta Jihar, Hajiya Asabe Balarabe ta ce, gwamnatin jihar ta ga dacewar samar da magungunan don inganta asibitocin da ake lura da yaran da suke fama da cutar yunwa da sauran cututtukan da suke da alaƙa da rashin lafiyayyen abinci mai ƙunshe da sinadaran ƙara lafiya.
Hajiya Asabe Balarabe ta ce, gwamnatin jihar ta riga ta fitar da maƙudan kudi don raba magungunan a dukkan manyan asibitocin jihar.
Kwamishinar ta ce, tuni Ma’aikatar Lafiya da hadin gwiwa da masu ruwa-da-tsaki suka shirya tsaf don tabbatar da abincin ya kai ga yaran da abin ya shafa.
Ta gargadi jami’an kiwon lafiya da kada wani ya kuskura ya karkatar da su domin duk wanda aka kama zai fuskanci hukuncin da ya dace.
A ƙarshe Hajiya Asabe Balarabe ta shawarci iyaye su yi amfani da wannan dama wajen inganta lafiyar ’ya’yansu.
Shi ma da yake jawabi, Daraktan Hukumar Kula da Rarraba Magunguna ta Jihar Sakkwato, Alhaji Umar Attahiru ya umarci malaman kiwon lafiya da ke cikin shirin su sa ido sosai wajen ganin yaran da ke fama da wannan lalura ce suka ci gajiyar shirin.
Kebbi
Yunwa ko rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara a Jihar Kebbi ya zama abin daga hankali ba kawai ga iyayen yara ba har da gwamnatin jihar domin a cikin ’yan watannin nan lamarin ya dada ƙamari da zamewa damuwa sosai saboda ƙarin yaduwar matsalar.
Wasu asibitoci da Aminiya ta ziyarta a Birnin Kebbi, hedikwatar jihar ta ga ana kula da yaran yadda ya kamata.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci ƙaramin asibiti da kea Badariya a Birnin Kebbi, yara tara ne kawai ke karɓar maganin, kusan hakan ne a sauran ƙananan asibitocin cikin garin da wakilinmu ya leƙa.
A’ishatu Buhari, wata mahaifiya da ta tattauna da wakilinmu ta ce ana kula da uku daga cikin ’ya’yanta biyar da ke fama da matsalar. Yaran su ne Ahmad dan shekarar 5 da Ibrahim, dan shekara 3 da Dauda dan shekara daya.
“Ba wani abin a-zo-a-gani da zan iya yi wa yaran nawa, saboda tsadar kayayyakin abinci. Ba za mu iya saya musu irin wannan nau’in abinci ba,” in ji ta.
Ta ce, tuwon masara ne kadai yaran ke ci a gida, wanda suke samu sau daya a rana, sai wani lokaci su sha fura. Ta ce ba ta samun isasshen ruwan nonon da take iya shayar da jaririnta.
Halima Aliyu, wata uwa mai kimanin shekara 26 da aka shawarce ta kan ta shayar da jaririyarta zallan ruwan nono na tsawon wata shida ta kasa kaiwa.
“A lokacin da take shekara biyu ne na lura da yadda cikinta ke kumbura yayin da jikinta ke yanƙwanewa.
“Da na kai ta asibiti ne suka ce ba ta samun isasshen abinci. Ni ban san yadda zan yi ba, don gaskiya ba mu da abincin da suka ce in riƙa ciyar da ita da shi,” in ji ta.
Wata ma’aikaciyar jinya a ƙaramin asibitin ta ce, wannan lalurar ce suke ta faman kula da ita a wannan lokacin a asibitin.
“Ina ganin iyaye mata na buƙatar shawarwari kan irin abin da za su riƙa ciyar da ’ya’yansu da shi.
“Bayan wannan kuma ƙuncin tattalin arziki da ake fama da shi ne babban abin da yake haifar da wannan matsala da take shafar ƙananan yara,” in ji ta.
A watanni kadan da suka gabata wata ƙungiya mai suna, CS-SUNN da hadin gwiwa da Asusun UNICEF suka bayar da alƙaluman yaduwar wannan cuta a jihar.
Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Kasafi da Tattalin Arziki ta jihar, Hajiya A’isha Usman ta ce adadin abin damuwa ne.
“Za mu sake duba lamarin don amfanin mutanen Jihar Kebbi. Za mu mayar da hankali wajen samar da abinci mai gina jiki a 2024,” in ji ta.
Mai Bai wa Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Ƙungiyoyi Masu Zaman Kansu, Alhaji Usman Buhari ya bayyana a taron manema labarai da CS-SUNN a Birnin Kebbi cewa gwamnatin jihar tana daukar ƙwararan matakai a kan matsalar domin gwamnatin Idris ta damu matuƙa a kan lamarin.
Zamfara
A Jihar Zamfara, cibiyoyin kiwon lafiya da ke Shinkafi da Zurmi sun samu ƙaruwar cutar ce da kaso 30 a watan Afrilu idan aka kwatanta da na watan Maris, yayin da Asibitin Talata Mafara, ta ƙaru da kaso 20.
Aminiya ta ruwaito a watan Disamban bara, yadda Ƙungiyar MSF ta kwashe wasu ma’aikatanta a jihar, lamarin da wasu ke ganin zai haifar da gagarumin ci baya a fannin kiwon lafiya musamman a karkara.
Mazauna garuruwan Bagega da Abare da Dareta da ’Yar Galma da Nasarawa da ke ƙananan hukumomin Anka da Bukkuyum suna cikin wadanda matsalar ta addaba a jihar.
Yawanci sun bayyana cewa janyewar ma’aikatan MSF daga asibitocin ta taimaka wajen dada dagulewar al’amura.
Wani mazaunin Bagega, Malam Hamisu Isyaku, ya tabbatar da ƙaruwar wannan matsala a tsakanin ƙananan yara a yankin.
Bauchi
A Jihar Bauchi ma akwai fargaba da damuwa na ƙaruwar yawan yaran da ke fama da wannan lalura a tsaka da halin matsi da ƙuncin rayuwa da ke fama da su sakamakon cire tallafin man fetur da faduwar darajar Naira.
Bincike ya nuna cewa daruruwan mata masu shayarwa kan cika cibiyoyin kula da masu matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki na ƙananan yara (IMAN) da aka ware a ƙananan asibitoci da ke ƙananan hukumomin Bauchi da Ganjuwa da Ningi.
Jami’in Sashen Lura da Abinci Mai Gina Jiki na Jihar Bauchi, Alhaji Abubakar Saleh, ya ce ƙananan yara 4,384 ke fama da matsanancin rashin lafiyar da ke alaƙa da yunwa aka kwantar da su a cibiyoyi 14 da ke fadin jihar.
Lokacin da wakilinmu ya ziyarci ƙaramin asibitin Kofar Ran da ke garin Bauchi, ya lura da yadda iyaye mata da dama da ke da irin wadannan yara masu dauke da matsalar ana kula da su a cibiyar.
Kuma sun bayyana cewa talauci da matsin tattalin arzikin da ake fama da su ne ke ta’azzara ƙaruwar cutar.
Haka da ya ziyarci Asibitin Yalwa da ke garin Bauchi ya ga yadda aka samu ƙananan yara kusan 400 da ke fama da matsalar rashin abinci mai gina jikin.
Jami’in da ke kula da sashen a asibitin, Malam Mukhtar Ahmad ya ce ana samun ƙaruwar masu wannan lalurar ce a tsakanin ƙananan yara sakamakon rashin samun abinci mai dauke da isassun sinadaran gina jiki.
Rahotanni daga: Lubabatu I. Garba (Kano), Olatunji Omirin (Maiduguri), Abubakar Auwal (Sakkwato), Ismail Adebayo (Birnin Kebbi), Yusha’u A. Ibrahim (Gusau) da Hassan Ibrahim (Bauchi) Fassarar Mohammed Ibrahim Yaba, Kaduna da Ahmed Ali, Kafanchan