Wani mutum wanda aka samu da laifi kuma aka yankewa hukunci kan aikata fyade a Maiduguri ya shaidawa kotu cewa yanzu ya sami matsala ba zai iya haihuwa ba lokacin da yake kokarin aikata fyaden a kan wata mata.
Kotun dai ta sami Jibrin Yuguda da Shuaibu Isa, wadanda dukkansu suka fito daga Karamar Hukumar Shani ta jihar Borno da laifin keta haddi, lamarin da ya saba da tanade-tanaden sassa na 85 da 285 na Kundin Manyan Laifuka na jihar.
- Abin da ya sa har yanzu ba mu biya ma’aikatan zaben Kano hakkokinsu ba – KANSIEC
- An kama magidancin da ya daba wa matarsa wuka a Anambra
An dai zarge su ne da afkawa wata mata wacce ke aiki a gonarta, inda suka turmusheta a kasa, suka cire mata kaya sannan suka sadu da ita ta karfin tsiya.
’Yan sanda masu shigar da kara dai sun shaidawa kotun cewa Jibrin, wanda shine ya kayar da matar a kasa kuma ya cire mata kaya ya gaza saduwa da ita sakamakon ya sami matsala a gabansa.
Daga nan ne ya ce sai ya bankare hannuwanta inda abokin laifin nasa, Shu’aibu ya yi mata aika-aikar.
Da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Gana Wakkil na Babbar Kotun Jihar Borno ya yi musu sassauci saboda masu shigar da kara sun gaza gabatar da hujjojin da za su gamsar da kotun cewa an aikata mata fyaden.
Ya ce shari’ar aikata fyade tana da matukar sarkakiya, sannan kuma masu shigar da kara sun gaza gabatar da rahoton likitan da zai tabbatar da aikata laifin, yayin da shi kuma likitan ya gaza bayyana a gaban kotun bayan dage shari’ar a lokuta daban-daban.
Ya ce aikata fyade na neman zama ruwan dare yanzu tsakanin al’umma, inda ya ce dole sai an dauki tsauraran matakai kafin a shaawo kan matsalar.
Daga nan sai alkalin ya yanke wa Jibrin hukuncin daurin shekara daya ba tare da zabin biyan tara ba, shi kuma Shu’aibu aka yanke masa hukuncin daurin shekaru uku ba tare da zabin tara ba.