✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda yin lalata tsakanin iyaye da ’ya’yan cikinsu ta zama ruwan dare

A wannan zamani, an kai matsayin da wasu iyaye sun dauki yin jima'i da ’ya’yan cikinsu ba a bakin komai ba.

Wata muguwar dabi’a da take ci gaba da naso a cikin al’aummar kasar nan, musamman a yankin Arewa, ita ce yadda iyaye ke yin lalata da ’ya’yan cikinsu.

Wannan al’amari ya yi munin da hatta tsakanin ’yan uwa ciki daya suke yin lalata da juna, ko tsakanin uwa da dan cikinta.

A zantawarsu da shirin Daga Laraba, wanda Aminiya ke gabatarwa ta intanet, wata majiya ta bayyana kaduwarta kan yadda wannan mummunar dabi’a ta yi katutu a cikin wasu iyalai, inda wa ke kwanciya da kanwarsa uwa daya, uba daya da kuma mahaifiyarsa, haka ma uban na kwanciya da ’yarsa.

“Wannan ita ce al’ummar da muke ciki a yanzu,” inji majiyar  zantawarta da shirin Daga Laraba.

Ta kara da cewa, matsalar ta kai inda za a kama uwa tana kwanciya da danta, amma sai ta ce gara hakan ta faru a tsakaninsu da ya je yana iskanci a waje.

Binciken Aminiya ya gano wannan muguwar dabi’a ta samu gindin zama a gidaje da dama, musamman a gidajen masu mulki da masu hannu da shuni.

Malam Hussaini Ahmad, babban jami’i a Hukumar Hisbah a Jihar Kano ya tabattar ana samun aukuwar wannan abin kazanta a cikin al’ummar jihar.

A cewarsa, “Muna samun ire-iren wadannan korafe-korafen — wa yana neman kanwa, uba yana mu’amala da ’yarsa, dan wannan dakin da dan wancan dakin alhali ubansu daya, masu uwa daya uba dayan ma akwai su.”

Har wa yau, wata majiya ta daban ta ce, “A kusa da mu ma ya taba faruwa mun gani.

“Musamman ma a gidan sarauta, za ka ga kanin uba yana bin ’yarsa, sannan daki da daki suna bin juna.”

Da yake karin haske kan kazancewar lamarin, Farfesa Sani Lawal Malumfashi na Jami’ar Bayero ta Kano, masanin halayyar dan Adam da zamantakewa, ya yi bayanin cewa, “Dabi’ar iyaye su mu’amalanci ’ya’yansu ta zama tsohuwar yayi; yanzu abin da ke faruwa shi ne musayar matan aure a tsakanin abokai.”

Game da dalilan da ke haifar da wannan kwamacalar, malamin ya ce har da mu’amalar aure tsakanin mata da miji a gaban ’ya’yansu da mutuwar aure da yankewar jama’i a tsakanin ma’aurata alhali ana tare da makamantansu.