✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda yanayin hazo a Kano ya kawo wa matafiya cikas

Yanayin hazon da aka tashi da shi a garin Kano da ma wasu jihohi ya hana jirage zuwa yankunan.

Tun daga ranar Juma’ar da ta gabata ce aka fara fuskantar yanayin sanyi mai dauke da hazo a Jihar Kano wanda hakan ya kawo cikas ga wasu matafiya a ciki da wajen Jihar.

A zantawar da Aminiya ta yi da wasu daga cikin matafiya daga Kano da kuma wadanda ke fitowa daga wasu wuraren da ke shirin shiga Jihar, sun bayyana ra’ayoyi masu kamanceceniya da juna.

Nafiu Maigari, wani matafiyi da ya gaza samun tafiya Abuja zuwa Kano, ya bayyana cewa “Na sayi tikiti tun ranar Juma’a zan je Kano, amma da na zo filin tashin jirage sai na samu cewa jirage ba su da damar tashi saboda yanayin da aka tashi da shi a Jihar Kano.

“Hakan ya sanya ni tafiya a mota, wanda ita ma tafiya ba dadi saboda yanayin hazo”, a cewar Maigari.

Shi ma wani fasinja, Bala Auwalu, da zai taso daga Kano zuwa Legas, ya bayyana yanayin da ya samu kansa.

“Tun da na samu labarin an tashi da hazo a ranar Asabar na san zan iya samun cikas a tafiya ta.

“Ko da na karaso filin jirgi sai na tarar da mutane na ta korafi kan yanayin da aka wayi gari da shi a Jihar Kano saboda yadda jirage suka gaza tashi,” in ji Auwalu.

Kazalika, wannan lamari ya sanya wasu manyan mutane da suka hada da gwamnoni da manyan jami’an gwamnati rashin halartar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar jigon APC, Bola Ahmed Tinubu wanda aka gudanar ranar Litinin a Fadar gwamnatin Kano.

Da aka tuntubi Kakakin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Saman Najeriya (FAAN), Misis Henrietta Yakubu, ta ce rashin kyawun yanayin ne ya hana jirage tashi zuwa jihohin da lamarin ya yi kamari.

%d bloggers like this: