✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ’yan takara ke cika wa daliget aljihu da kudade

Da alama kasuwar daliget ta bude a yayin da ’yan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’aiyyar adawa ta PDP ke…

Da alama kasuwar daliget ta bude a yayin da ’yan takarar shugabancin kasa na Jam’iyyar APC mai mulki da babbar jam’aiyyar adawa ta PDP ke zawarcinsu.

A halin yanzu, gabanin zaben fitar da ’yan takarar jam’iyya, masu neman kujerar shugaban kasa na bin deleget suna cika musu lalita da kudade don neman kuri’unsu.

Badakalar N80bn: Ministar Kudi ta kori Akanta-Janar, Ahmed Idris

’Yan takara 38 ne ke neman takarar shugaban kasa karkashin manyan jam’iyyun biyu; APC ’yan takara 23, ita kuwa PDP mutum 15.

Daga ranar 30 ga wannan wata na Mayu zuwa 1 ga watan Yuni deleget 7,800 da aka zabo daga sassan kasar nan za su yanke hukunci kan makomar ’yan takarar APC 23 da jimillar.

Daliget 3,700 ne za su kada kuri’a don tsayar da dan takara daya daga cikin mutum 15 da ke neman tikitin PDP domin fafatawa a babban zaben 2023.

Kafin zaben fid da gwanin, ’yan takarar na ta zarya a jihohi suna tuntubar daliget tare gwangwaje su da kudade da sauran kyaututtuka daban-daban.

Rahotannin da wakilanmu suka tattaro na nuni da cewa daliget na samun abin arziki daga hannun ’yan takarar.

Wani deleget ya shaida wa Aminiya cewa a irin wannan lokaci ne kasuwarsu ke ci, kuma suna samun kudi sosai.

A makon jiya mun kawo rahoto na musamman kan yadda Dala tai tashin gwauron zabo, saboda yadda masu neman takara ke neman ta ido rufe, gabanin zaben fidda gwanin jam’iyyun siyasa.

Manyan ’yan takarar da suka karade kasar nan domin neman goyon bayan daliget karkashin inuwar Jam’iyyar APC sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Uban Jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da tsohon Ministan Sufuri Rotimi Amaechi, sai kuma Kayode Fayemi.

A bangaren PDP kuwa, akwai Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike da Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal da Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Sauran su ne Gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.

Akwai kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi da kuma hamshakin dan kasuwar nan, Mohammed Hayatu-Deen.

Osinbajo a Kano, ya bukaci lambar bankin daliget

A ranar Talata Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ziyarci Jihar Kano domin ganawa da wakilan Jam’iyyar APC.

Taron wanda ya gudana a dakin taro na Coronation da ke gidan gwamnatin jihar, ba a bai wa ’yan jarida damar shiga ba.

Wani jami’in tsaro ya shaida wa manema labarai cewa “Umarni ne daga sama” a kan hakan.

Sai dai Aminiya ta lura cewa bayan an tantance daliget din, wani jami’in tawagar Osinbajo yana karbar bayanan asusun ajiyar bankinsu.

An kuma ji daya daga cikin wakilan yana cewa “Ba tsaba ba ne, an tura sun shiga asusun banki.”

An ce shi ma Wike da ya ziyarci Kanon, ya bayar da sabuwar mota ga shugabannin jam’iyyar.

Shugaban PDP a Gombe ya samu mota, wakilai sun dara da ganin ‘alat’

A Jihar Gombe kuwa, wasu ’yan takarar shugaban kasa hudu ne daga APC da PDP suka ziyarci jihar suka tattauna da daliget.

Osinbajo da Tinubu da Fayemi ne suka ziyarci a matsayin ’yan takarar APC, yayin da Wike da Bala Mohammed da Tambuwal da Udom Emmanuel suka shiga jihar daga bangaren PDP.

Wike shi ne ya fara shiga jihar a watan Afrilu, ya gana da shugabannin jam’iyyarsu tare da rakiyar tsohon Gwamna Jihar, Ibrahim Hassan Dankwambo.

Wani daliget da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, Wike ya sanar da bayar da sabuwar mota ga shugaban Jam’iyyar PDP na jihar.

Haka nan, a cewar wani daliget din kuma kowanne daga cikin masu neman takarar shugabancin kasa ya bayar da makudan kudaden da aka raba wa daliget.

An bayyana cewa, a lokacin da Bala Mohammed da Tambuwal da Udom suka ziyarci jihar, kowannensu ya bayar da kudi da aka raba tsakanin shugabannin jam’iyyar da daliget.

Haka su ma bangaren APC, ’yan takara ukun da suka ziyarci jihar, Osinbajo da Tinubu da Fayemi, an ce sun raba wa deliget kudi.

Kaduna: Tinubu ya bai wa daliget N60m, Amaechi N20m

Da dama daga cikin ’yan takara suna zawarcin inda suke bayar da kudade masu tsoka ga daliget don samun kuri’arsu.

Wakilan Kaduna sun ce suna jin su tamkar sarakuna ne su, domin masu neman shugabancin kasa na rawar jikin neman ganawa da su.

A Jam’iyyar APC, manyan ’yan takara biyu, wato Tinubu da Amaechi, tuni suka ziyarci daliget din tare da raba musu kudade masu yawa.

Yayin da Tinubu ya bayar da Naira miliyan 60, Amaechi kuma ya su Naira miliyan 20.

Daga Jam’iyyar PDP kuwa, Wike da Bala Mohammed da Saraki da sauran ’yan takara sun kai ziyara.

Daliget sun ce babu wani abu da aka ba su kai-tsaye duk da cewa Wike ya bayar da tallafin Naira miliyan 200 ga ’yan gudun hijira a Kaduna.

Daliget sun dara a Binuwai

A Jihar Binuwai kuwa, wakilan jam’iyyun biyu sun dara ganin yadda aka cika musu lalitarsu da sulalla.

Wakilinmu ya jiyo wasu daliget na cewa kudaden da suke samu a halin yanzu daga masu neman takarar shugaban kasa da na gwamna, sun cire su daga halin kuncin tattalin arziki tare da iyalansu.

“Za mu ji dadin arzikin da muka samu,” a cewar daya daga cikin daliget din.

Duk da cewa a ranar Talata ’yan takarar APC suka fara shiga jihar, wadda Tinubu ya bude fage, amma har zuwa yanzu ba a san ko nawa deleget din za su samu ba.

Sai dai an ce Osinbajo ya aike da ’yan tawagarsa makonnin baya inda kowane deleget ya samu Naira 50,000.

Ana sa ran Osinbajo zai ziyarci daliget din jihar a cikin wannan makon.

A bangaren Jam’iyyar PDP, biyu daga cikin wakilan da suka zanta da wakilinmu sun tabbatar da cewa suna samun Naira 250,000 ko sama da haka daga hannun ’yan takarar Shugaban Kasa da suka kai musu ziyara.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Gwamna Bala Mohammed da Saraki da Wike da Mohammed Hayatu-deen da Tambuwal da Atiku duk sun ziyarci jihar.

‘Rashawa babbar illa ce ga dimokuradiyya’

Da take tsokaci game da irin wannan halayya, Daraktar Cibiyar Dimokuradiyya da Cigaba (CDD), Idayat Hassan, ta ce zaben Najeriya, zabe ne na kudi; Don haka kudi ke bayyana tsarin dimokuradiyyar kasar.

A cewarta, sayen kuri’un daliget ya zama al’ada a zabukan da suka gabata, har da zaben 1993 da ake ganin shi ne mafi inganci a tarihin Najeriya, an ga yadda ake sayen kuri’u a lokacin zaben fid da gwani.

“A 2015 mun ga yadda aka sayar da kuri’u tsakanin Dala 2,000 zuwa dala 3,000 a lokacin zaben fid da gwani na Jam’iyyar APC a Legas inda ’yan takaran suka kashe tsakanin Dala miliyan 16 zuwa 24.

“Zaben fid da gwani na PDP a 2019 bai bambanta ba inda aka rinka sayen kuri’a tsakanin Dala 2000 zuwa 10,000 a Fatakwal.

“Ba wa deleget rashawa shi ne babban abin da ya fi daure kai wajen cin hanci da rashawa a lokutan zabukan wanda haka ne ke hana a tsayar da wadanda suka cancanta.

“Zaben bana na iya zama mafi muni a zaben fid da gwani saboda yadda ake kashe makudan kudade wajen neman kuri’u.

“Akwai babban aiki dangane da aiwatar da doka da kuma tsarin da ya kamata a bi don dakile rawar da kudi ke takawa a siyasa,” inji ta.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Shugaban Gamayyar Inganta Tsarin Zabe, (PER), Ezenwa Nwagwu, ya ce ya kasance al’adar manyan jam’iyyun siyasa su “Sayi kuri’un daliget saboda a tunaninsu hakan ne zai ba su nasara.

“Abin da yake faruwa a halin yanzu kamar bin sawu ne, domin da kyar duk wani taron jam’iyyun siyasa tun daga 1998 har zuwa yau, ba wanda ba a yi mu’amala da kudi ba.

“Daliget da shugabannin jam’iyya sun kasance tamkar ’yan kasuwa a irin wannan lokaci,” in ji Nwagwu.

A nasa bangaren, Babban Darakta mai kula da harkokin kare hakkin dan Adam da ilimin jama’a (CHRIceD), Dakta Ibrahim Zikirullahi, ya ce yin amfani da kudi wajen jawo daliget abu ne da bai dace ba.

Har ila yau, Shugaban Kungiyar Sa ido Kan Harkokin Zabe (TMG) kuma Babban Darakta na Cibiyar Kare Hakkin Jama’a (CISLAC), Malam Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana cewa shigowar kudi a siyasa yana da illa ga dimokuradiyya da ma kasa baki daya.

Ya ce hakan na nuni da ’yan siyasa suke da tasiri a kan daliget.

 

Daga Ismail Mudashir, Abbas Jimoh (Abuja), Clement A. Oloyede (Kano), Haruna G. Yaya (Gombe), Hope A. Emmanuel (Makurdi), Lami Sadiq (Kaduna) & Magaji l. Hunkuyi (Jalingo)

%d bloggers like this: