Sababbin ’yan sandan da aka dauka a farkon 2020, sun bayyana yadda suka shafe wata bakwai a cikin aiki ba tare da an biya su ko da sisin kwabo ba.
Wadansu matasa da suka yi nasarar shiga aikin dan sandan da Aminiya ta nemi zantawa da su, sun ce hakan na faruwa ne bayan sun kashe kudi mai yawa a yayin ba su horo, da ba zai gaza Naira dubu 300 ba.
- A kori Fashola: Ba abin da ya yi a Arewa —NEF
- Arewa ta fi ko’ina hatsari a Najeriya —Sarkin Musulmi
- Ba a ware wa tashar Mambila ko sisi ba
“Mun kai kamar mutum 12 da aka dauka daga karamar hukumarmu, sannan aka tura mu garin Ilorin a Jihar Kwara, tare da wadansu daga wasu yankuna.
“A can ne rukuninmu ya samu horo. Yau a tambayi kudin abu kaza gobe na wani abin, adadin kudin da aka karba daga wajena ba zai gaza Naira dubu 300 ba, idan aka hada baki daya,” inji daya daga cikinsu.
Sababbin ’yan sandan wadanda aka gaza biyansu albashi na wadannan watanni sun kuma koka kan irin yadin da ake ba su don su dinka kaki, inda suka ce da alama yadin ya kwana biyu ko kuma ba mai inganci ba ne.
Sun ce yadin ya kode cikin kankanen lokaci. “Kaki daya ne kadai muke sawa kuma a kullum sai mun zo aiki a ofishin ’yan sanda da aka tura mu, inda muke isowa wurin aiki da misalin karfe 8:00 na safe, mu tashi karfe 6:00 na yamma.
“Wannan kaki da ka gani mai kyau a jikina da kudina ne na saye shi ba wanda aka ba ni ba ne,” inji shi.
Daya daga cikin ’yan sandan ya ce a dalilin gaza biyan kudin mota daga garinsu zuwa ofishin da ake bukatar ya je a kullum, a yanzu ya gwammace ya kwana a daki guda da yayarsa da ke aure a inda yake aikin, da kuma samun abincin dare a gidan.
Ya ce sun dogara ne daga taimakon kudi da suke samu daga wajen manyansu a ofishin don magance bukatun da suka zama dole kamar cin abinci a wajen aiki.
“A yanzu haka ba ni da lafiya, ba ni kuma da kudin da zan yi jinya, sannan fashin zuwa wurin aiki na iya kai ni ga rasa aikina duk da a ba biyan mu alabshi”, inji shi.
Wata ’yar sanda sabuwar dauka, ta ce daga gidan iyayenta take zuwa ofishin a duk yini inda take kashe kimanin Naira 800 zuwa da dawowa.
Za a biya su duk abin da suke bi a Nuwamban nan –Hedkwatar ’Yan sanda
Da Aminiya ta tuntubi Babban Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Frank Mba ya ce za a biya sababbin ’yan sandan daukacin albashinsu da suke bi.
“Na san ba za ka rasa sanin matsalar da ta shafi daukarsu aiki ba. Wadansu sun bi ta bayan fage wajen ganin sun shiga aikin, to wannan da sauran wasu matsaloli da suka bijiro suka tilasta jinkirta fara biyan su albashi har zuwa wannan lokalci da aka tantace lamarin.
“Mun damu matuka da halin da suka shiga, ba wanda ya ji dadin haka kuma hakika sun nuna juriya da biyayya tare da aiki duk da kasancewa a cikin wannan hali.
“Amma za a biya su kudin a wannan wata mai karewa”, inji shi.