✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan sanda suka cafke ’yan kungiyar asiri

Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa reshen Jihar Legas ta ce tana ci gaba da titsiye wasu mutum biyu bisa zargin zama ’yan wata kugiyar matsafa…

Rundunar Yan Sanda ta Kasa reshen Jihar Legas ta ce tana ci gaba da titsiye wasu mutum biyu bisa zargin zama ’yan wata kugiyar matsafa mai suna Aiye bayan ta cafke su.

’Yan sanda sun kama matasan ne suna tsaka da tattaunawa a wani otal a Shasha, a kokarinsu na kai harin ramuwar gayya kan wasu abokan takun-sakarsu.

Kakakin Rundunar a Jihar Legas, Bala Elkanah ya ce sun kwace bindiga samfurin fistol kirar gida daga hannun matasan.

Elkanah ya ce da misalin karfe 5:30 na ranar 23 ga watan Yuli rundunar ta samu bayanan sirri cewa matasan dauke da makamai na taro a otal din.

Jim kadan da samun rahoton ne jami’ansu a ofishin ’yan sanda na Shasha da hadin gwiwar rundunar yaki da ’yan fashi na SARS suka bazama domin kama su.

Kakakin ya ce, “Da suka hango jami’an tsaron sai suka yi yinkurin tserewa, duk da yake mun samu nasarar cafke mutum biyu daga cikinsu.

“Mun sami kwace bindigogi kirar gida a hannunsu da kuma harsasai. Muna fadada bincike don kama ragowar mutanen”, inji Elkanah.