’Yan Najeriya na rokon Gwamnati ta kara wa’adin da ta sanya na mako biyu su yi wa layukan wayoyinsu rajista da lambar shaidarsu ta dan kasa (NIN).
Kiraye-kirayen sun fito ne daga mutanen da suka yi dandazo domin yin rajitsar shaidar dan kasa a ofishin Hukumar Bayar da Shaidar Dan Kasa (NIMC) da ke Legas.
“Karfe 4:30 na asuba na kawo iyalaina kuma wannan shi ne karo na biyu a cikin mako guda”, inji wani dan kasuwa mai suna Sunday Jegede.
“Ya kamata a kara wa’adin da da sanya domin na lura ita kanta hukumar da ke akin ba ta shirya ba; wahalar da ’yan Najeriya kawai take yi.
“Duk da sammakon da na yi na baro gida da lokacin da na iso nan, amma wai ni ne mutum na 32,” inji shi.
Shi ma wani dan kasuwa, Kingsley Onwujulugba ya ce: “Tun karfe 5:15 na asuba na iso nan, yanzu 6:30 na safe amma har yanzu ba a ba ni lamba ba a kan layi.
“Ya kamata su kafa cibiyoyin yin rajistar saboda wahala kawai jama’a suke sha; a samu akalla kowace karamar hukuma ta samu cibiyar yin rajista.
“Hakan zai taimaka ya saukaka wahalhalun yin dogauwar tafiya kafin da jama’a ke yi domin su samu rajista kafin cikar wa’adin.
“Ni tsoho ne ba na iya tsayuwa na lokaci mai tsawo ba, ga shi ba a tanadi wurin zama domin tsofaffi da ko mata masu ciki ba.”
‘Lambar NIN ta zama dole’
Wata ’yar kasuwa, Misis Oyeniyi Chinyere ta ce tun da dadewa ta yi rajista, yanzu dai ta zo ne ta karbi lambarta ta (NIN).
Bukatar samun katin shaidar dan kasa ta sa daruruwan ’yan Najeriya asubanci zuwa ofisoshin NIMC su kama layin don yin rajista.
A makon jiya ne Ma’aikatar Sadarwa ta sanya wa’adin mako biyu ga duk masu amfani da wayoyin sadarwar a Najeriya su tabbata sun yi wa layukan rajista da lambarsu ta NIN.
Hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa a Najeriya, ta umarci kamfanonin waya su toshe duk layin wayan da ba shi da lambar NINI, da zarar wa’adin ya cika a ranar 30 ga watan Disamba, 2020.
Tun farko ta ba da umarnin hana sayar da sabbin layukan waya da yi musu rajista, a wani mataki na kokari yi wa tufkar miyagun laifuka hanci.
Majalisar Wakilai dai ta bukaci NCC da ta kara wa’adin sati biyun da ta sanya na yi wa layukan waya rajista ta lambar NIN ya koma sati 10.
Majalisar ta ce wa’adin bai dace ba saboda an sanya shi ne a daidai lokacin da mutane ke shirye-shiryen tafiye-tafiyen hutun karshen shekara.
Ta kara da cewa rufe layukan cikin sati biyu zai kasance ne a lokacin da mutane da dama ba su samu halin yi ba, kuma hakan zai jefa yawancin mutane cikin karin damuwa baya ga wadda suke ciki.
Tun da farko dai Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami ne ya umarci a rufe layuka marasa rajista bayan Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya sun dora laifin ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane a kan yawaitar layukan waya da aka riga aka yi wa rajista.
Manyan Hafsoshin sun yi korafin ne a zaman da suka yi da Shugaba Buhari, wanda ya nuna fushinsa kan ci gaban ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane musamman a yankin Arewa maso Yamma.
A wancan lokaci, Buhari ya bayyana musu cewa ba su da wani uzuri kan ci gaban matsalar, abin da ake gani tambar alama ce ta shirinsa na tisa keyarsu.
Ya kuma umarce su da su yi aiki tare da Pantami domin yi wa tufkar hanci.