Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe da ‘yan Majalisar guda 4 sun kamu da coronavirus.
Shi ma Kwamishinan Ruwa da Albarkatun Kasa Mijinyawa Yahaya ya kamu da cutar.
Kwamishinan ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook.
Tuni aka killace Shugaban Majalisar, Abubakar Sadiq Ibrahim Kurba, da takwarorin nasa da sakamako ya nuna sun harbu da cutar.
Wata majiya da ta shaida wa wakilinmu cewa an killace Shugaban Majalisar da sauran ‘Yan Majalisar ne a cibiyoyi daban-daban na killace masu dauke da cutar a jihar.
Ta kara da cewa an dauki jinin iyalan dukkan ‘yan majalisar domin yi musu gwajin cutar.
A makon jiya ne Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ya umurci Kwamishinonin sa da masu ba shi shawara da hadimansa da yan majalisar jihar da ma daukacin ma’aikatan gidan gwamnati da su mika kansu domin yin gwajin cutar.
Sakataren gwamnatin jihar Farfesa Ibrahim Njodi shi ya jagoranci tawagar ma’aikatan gidan gwamnatin a ranar Alhamis don yin gwaji.
Umurnin gwamnan ya biyo bayan mutuwar wani Darakta a Ofishin Sakataren Gwamnatin jihar, Shu’aibu Danlami wanda bayan mutuwarsa aka gano cutar coronavirus din ce ta kashe shi.