✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ‘yan kasashen waje ke zuwa koyon Harshen Hausa a Jami’ar Bayero

Kamar yadda kuke gani mun zo nan don mu koyi Harshen Hausa da al’adun Hausawa.

Marka da Nafisa da Habiba da Larai da Baraka da Zahra dukkaninsu ‘yan kasar China (Sin) ne, duk cewa suna da sunayensu na asali, amma sun zabi a kira su da wadannan sunaye ne don irin sha’awar da suke da ita a harshen Hausa.

Garba, wanda sunansa na asali Gabor Gabor Henry Raschberger dan kasar Jamus ne shi ma yana tare da wadancan mata, inda suke koyon harshen Hausa a Jami’ar Bayero.

Jami’ar Bayero na daya daga ciki jami’oin da suka samu karbuwa a wasu kasashen duniya.

Har ila yau kuma Allah Ya albarkaci jami’ar da samun masu neman gurbi don yin karatu da neman ilimi a cikinta.

Wani abu da ke kara wa jami’ar farin jini da karbuwa shi ne daya daga cikin harsunan da ake koyarwa a jami’ar, wato harshen Hausa.

An dauki tsawon shekaru Jami’ar Bayero na yaye daliban da ke zuwa daga kasashen waje domin nazarin harshen Hausa, wanda Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya ke tarba a matsayin baki.

Wadannan dalibai suna yin shiga ta Hausawa wacce ke nuni da al’adun Hausawa.

Idan suna tare da dalibai ‘yan uwansu babu abin da za ka iya bambance su, sai dai ta launin fatar jikinsu.

Yayin da suke jawabi game da zamansu a jihar da kuma yanayin wurin da suke karatun, daliban sun nuna gamsuwarsu da yadda suke zaune.

Sun bayyana cewa, sun zo Nijeriya da Jami’ar Bayero ne don su koyi Harshen Hausa sakamakon sha’awar da suke da ita a kan harshen.

“Kamar yadda kuke gani mun zo nan don mu koyi Harshen Hausa da al’adun Hausawa.

“Za mu ci gaba da koyon al’adun Hausawa kafin mu bar kasar nan, mu koma kasashenmu.

“Gaskiya mun samu darasin rayuwa don mun koyi sababbin abubuwa da ba mu taba ji ko karantawa ba.

“ Kun san mun zo ne daga kasashe daban-daban don haka muna amfani da bambance-bambancen da ke tsakaninmu domin muna son hakan.

“Jami’ar tana kula da mu sosai. Tana ba mu kulawa ta musamman fiye da sauran daliban.

“Mun gode. Mun koyi saka sutura kamar Hausawa, mun koyi waka mun iya karin magana da wasu abubuwa masu yawa da suke da amfani,’’in ji su.

Sun kara da cewa, ba wai sun zo Kano don kawai su koyi Harshen Hausa ba, suna neman hanyoyin da za su iya yin aiki a wurare dabandaban.

Da yake magana da Aminiya, daya daga cikin malaman da ke koyar da su, Malam Kamilu Dahiru Gwammaja ya bayyana cewa, Harshen Hausa na kara samun tagomashi a cikin da wajen kasar nan.

Ya kuma bayyana cewa, daliban suna kokari sosai domin yanzu suna iya karatun Hausa. “Allah Ya albarkaci harshen Hausa da abubuwa masu yawa.

“Harshen ne mai saukin koyo. Haka kuma harshe ne da ke kara bunkasa a kullum, shi ya sa za ku ga mutane daga sassa dabandaban na fadin duniya suna sha’awar harshen.

“Masana na cewa harshen Hausa shi ne harshe na 11 mafi girma a fadin duniya. Haka kuma a nan Afrika babu harshen da ya kai shi saurin yaduwa.

“Wannan ne ya sa ake samun dalibai da suke zuwa don koyon harshen. Kamar yadda kuke gani, muna da dalibai daga Hamburg ta kasar Jamus da kuma Bejin ta kasar China (Sin).

“Wadannan dalibai suna kokari kwarai da gaske domin wannan ne abin da ya kawo su.

“A halin yanzu tuni sun fara sadarwa a tsakaninsu da yin rubutu da yin karin magana, kai har da wakoki suke yi a harshen,” in ji Dahiru.

Jami’ar Bayero ita ce jami’ar farko da ta fara bayar da digiri a harshen Hausa.

Haka kuma duba da yadda ake samun ‘yan kasashen waje suna kokarin koyon darussan harshen Hausa ka san harshen ya tumbatsa.

Ana magana da Harshen Hausa sosai a Arewacin Nijeriya kuma akwai makarantu da cibiyoyin ilimi da ke yi wa masu koyon harshen gata.

Harshen Hausa na daya daga cikin harsuna dangin Chadi, wanda ke cikin rukununin harsunan Afroasiantic, kamar yadda shafin Wikepedia ya bayyana.

Haka kuma harshe ne da ake amfani da shi a wurare da dama na fadin duniya, inda Hausawa ke magana da shi a Arewacin Nijeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Binin da Togo da bangaren Kudancin Nijar da Chadi da Sudan Binciken ya nuna cewa, fiye da mutane miliyan 50.7 ne ke magana da harshen Hausa a matsayin harshen farko wato na uwa.

Haka kuma akwai mutane miliyan 26.2 da suke magana da hashen a matsayin harshe na biyu. Idan aka hada za a samu mutane miliyan 77 da ke magana da harshen a duniya.

Mafi yawan masu magana da harshen Hausa suna zaune a Arewacin Najeriya da kuma Kudancin Nijar.

A Najeriya wuraren da ake magana da harshen Hausa sun hada da Kano da Katsina da Daura da Zariya da Gobir, wadanda suka sami kansu a cikin Daular Sakkwato bayan kammala Jihadin Shehu Usman Dan fodiyo a farkon karni na 18.

Harshen Hausa yana da kare-karen harshen yanki, wanda ke kunshe da bambance-bambance wajen furuci da kuma kalmomi.

A wasu lokuta ma mutum zai iya gane bambanci tsakanin karin harshen gabas da ya hada da Kano da na wasu wurare kamar Zariya da Bauchi da Daura da kuma karin harshen Kudu da ya hada da Sakkwato da Katsina da Gobir da kuma Arewacin Nijar.

Baya ga karin harshen yanki, akwai daidaitacciyar Hausa, wadda Kananci ya fi mamayewa, duk da cewa hatsin bara ne.