✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan IPOB suka sare kan abokin aikinmu suka kone gawarsa — Dan sanda

Yau kwana shida babu wani jawabi ko tuntuba da aka yi mana a hukumance.

Wani abokin aikin daya daga cikin ’yan sandan Kungiyar IPOB masu neman kafa kasar Biyafara suka kashe suka sare kawunansu sannan suka kone gawarwakinsu ya bayyana yadda ’yan ta’addar suka hallaka abokin aikinsu Sufeto Rufa’i Adamu.

Dan sanda wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa da safiyar ranar Alhamis din makon jiya da misalin karfe 7:00 na safe ne ’yan sandan cikin jerin gwanon motoci uku suka nufi filin jiragen sama domin su tarbi mutumin da suke yi wa aikin tsaro mai Kamfanin Sufurin Motoci na Young Shall Grow.

A cewarsa, “Sun taso ke nan, ina zargin an bai wa ’yan ta’addan bayanin suna tafe, sai suka yi musu kwanton-bauna suka bude musu wuta.Motar da marigayin yake ciki ita ce a gaba.

Sai ragowar motoci biyu na baya suka juya suka samu mafaka a ofishin ’yan sanda da ke kusa, amma abin mamaki da takaici har ’yan ta’addan suka kashe su, suka cire kawunasu suka kone gangar jikinsu ’yan sanda ko wadansu jami’an tsaro ba su kai masu dauki ba, duk da cewa labari ya iske su.”

Ya ce, “Da an kai dauki ko ba komai za a karbo gawarsu a cimma ’yan ta’addar, amma abin mamaki babu wani yunkurin da aka yi na far wa ’yan ta’addar, haka suka yi abin da suka ga dama suka wulakanta gawarwakinsu.”

Rufa’i Adamu da ‘yan IPOB suka kashe suka kone gawarsa

’Yan ta’addan IPOB sun far wa ’yan sandan ne a Jihar Anambra suka yi musu kisan gilla suka kone gawarwakinsu bayan sun cire musu kai, sannan suka yi bidiyo suka watsa a kafafen sada zumunta.

Matarsa da ’yan uwa da abokan arziki, wadanda suke cikin alhinin kisan gillar da aka yi wa Sufeta Rufa’i Adamu sun yi wa Aminiya bayani kan lamarin.

Uwargidan marigayin, Fa’iza Amadu Barau ta ce mijinta yana cikin ’yan sanda 14 da ke ba da tsaro ga mai Kamfanin Sufuri na Young Shall Grow.

“Su 14 ne, idan bakwai suka yi aikin kwana uku, sai bakwai su canje su, don su komo gida su huta.

“To a ranar Lahadi ya fada min cewa mai kamfanin na Young Shall Grow zai je garinsu a Anambra wajen bikin binne gawa.

“Ya fada min an ce idan suka isa can ko katin waya kada mutum ya fita nema domin garin ba tsaro. Sai na yi masa addu’a da fatar Allah Ya kare su.

“A ranar Talata ya dawo gida ya fada min za su tafi ranar Laraba da sassafe, domin a mota za su tafi yayin da mai kamfanin zai je ranar Alhamis ta jirgin sama su tare shi.

“Sun isa Jihar Anambra ranar Laraba, mun yi waya da shi a ranar da misalin karfe 10 na dare.

“Da gari ya waye ranar Alhamis na kira lambarsa ta ki shiga, sai da Magariba na samu labarin rasuwarsa.

“Na ga bidiyon kisan gillar da aka yi masa, babu abin da zan ce sai Innahlillahi wa innah Ilaihi raji’un, Allah zai saka mana abin da suka yi masa, Allah zai isar mana,” inji ta.

Ta ce tun bayan kisan da kona gawar da ’yan ta’addan suka yi har zuwa ranar Talata da take tattaunawa da Aminiya rundunar ’yan sandan ba ta tuntube ta ba.

“Yau kwana shida babu wani jawabi ko tuntuba da aka yi mana a hukumance.

“Dan uwansa wanda shi ma dan sanda ne ya sanar da mu rasuwarsa, amma babu wanda ya zo ya ce mana uffan a hukumance, haka mai Kamfanin Young Shall Grow bai ko aiko mana da ta’aziyya ba,” inji ta.

Fa’iza ta ce mijinta mutum ne da babu ruwansa da duk wani abu da babu gaskiya a ciki, ba ya cin hanci ba ya shiga kowace irin badakala, don haka da albashinsa ya dogara.

“A farkon bana ya zama Sufeta, a wannan lokaci ma ba a biyansa albashinsa na Sufeta ana yanke masa Naira dubu 40, sai daga baya ya yi ta bi har Allah Ya sa aka gyara aka daina cire masa wannan kudi, a lokacin Naira dubu 50 yake samu a albashin, bai fi wata uku ba da gyara matsalar,” inji ta.

 

Matar marigayin Fa’iza Amadu Barau tare da ‘ya’yansa hudu

Ta ce, “Shi dan asalin Jihar Adamawa ne amma muna zaune ne a nan Agege a gidan haya, iyayensa sun rasu, ina fata gwamnati za ta bi mana hakkinmu ta bai wa ’ya’yansa kulawa.”

Wani mai suna Malam Hassan ya ce marigayin abokinsa ne da suka shafe sama da shekara 8 suna zumunci a garin Agege.

Ya ce a duk ’yan sandan da yake mu’amala da su bai taba ganin natsattsen mutum, mai kirkin gaske kamar Sufeta Rufa’i ba.

“Mutum ne mai saukin kai da ba ya son hayaniya. Yawanci mutane sun san shi ne a masallaci, ba za su ce dan sanda ba ne don ba ya nuna kansa. Idan yana gida za ka ga yana taya iyalinsa hidimar gida.

“Mutum ne mai gaskiya a safiyar ranar da za su tafi aikin da ba zai dawo ba na hange shi a Masallacin Lawal Atana da ke Unguwar Oniwaya a Agege a lokacin Sallar Asuba.

“Da shi ake Sallah a duk lokacin da yake gida da shi ake yin sauran karatuttuka tabbas mun ji takaicin irin kisan gillar da ’yan IPOB suka yi masa.

“Muna fata gwamnati za ta kamo su a yi hukunta su, muna fata gwamnati ta kula da iyalansa ta dauki nauyin wahalhalunsu,” inji shi.

Shugaban Kwamitin Marayu na Legas a karkashin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah, Alhaji Umar Atana ya koka ne kan kisan gillar da aka yi wa dan sandan.

“Ni ban ma san dan sanda ba ne sai bayan da Allah Ya yi masa rasuwa. Nan yake zuwa muna Sallah, mutumin kirki ne mai saukin kai. Ya kawo min zuma na saya, rabuwa ta da shi ke nan, a gaskiya muna cikin takaici da jimamin kisan gillar da suka yi masa, kuma muna fata gwamnati za ta dauki mataki domin ’yan ta’addan ba su fi karfin gwamnati ba, abin takaici shi ne ko gawarsa ma ba su kyale ba balle a kawo ta mu sallace ta yadda Musulumci ya tsara,” inji shi.

Umar Atana ya ce sun fara nema wa iyalin marigayin tallafi domin suna bukatar taimako.

“Yanzu haka mun kai masu buhun shinkafa biyu, da kayan cefane, muna fata gwamnati ta zo ta tallafa wa iyalansa domin ya bar yara kanana guda hudu” inji shi.

A ranar Litinin, Ministan Labarai da Sadarwa Alhaji Lai Mohammed ya sha alwashin za a kamo tare da hukunta masu hannu a kisan gillar.

Ya ce al’amarin ya rutsa da ’yan sanda uku da suka hada da ASP Francis Idoko mai lambar aikin dan sanda (AP No.154945) da Sufeta Emmanuel Akubo, mai lamba (AP No.222336) sai Sufeta Rufa’i Adamu mai lamba (AP. No. 285009).

Ya ce dukkansu ’yan sanda ne da ke kan ganiyar aiki, kuma wadanda suka yi masu ta’asar sanannu ne ’yan Kungiyar ESN ta IPOB a karkashin jagorancin shugabansu Chinonso Okafor, wanda aka fi sani da TEMPLE.

Ya ce sun yi aika-aikar ce a ranar 27 ga Nuwamban bana. Alhaji Lai Mohammed wanda ya bayyana haka a Legas ya ce biyu daga cikin ’yan sandan da lamarin ya rutsa da su an yi masu kisan gilla wadanda suka hadar da Sufeta Akubo da Sufeta Adamu.

Kamar yadda bayani ya gabata har zuwa lokacin hada wannan rahoto Rundunar ’Yan sandan Najeriya da mai Kamfanin Young Shall Grow ba su tuntubi iyalin Sufeta Rufa’i Adamu a kan rasuwarsa ba, kuma ba su aike masu da wani jawabi da ya danganci hakan ba.