Masu gudun hijirar da ’yan bindiga suka koro daga Karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja da dama sun kama sana’o’in sayar da shayi da wankin motoci a domin samun kudin shiga a Minna, babban birnin jihar.
Guda daga cikinsu mai suna Nura Salisu, ya bayyana wa Aminiya cewa da wankin motar da yake yi, ya kan samu Naira 30,000 a wata.
- Saruniyar Denmark ta kamu da COVID-19 bayan halartar Jana’izzar Sarauniyar Ingila
- Yadda gizo-gizo a jana’izar Sarauniyar Ingila ya tayar da kura
“Duk da haka ina fargabar komawa garinmu, kogi ne kadai ya hana ’yan bindigar tsallakowa yankinmu na Rafi.
“Sai dai nakan je gida duk ranar Juma’a na dawo Lahadi.
“Daidai da manoma na fargabar girbi, domin kogin na kafewa, dole su gudu daga garuruwansu.
Shi ma wani, Jibrin Muhammad da ke sana’ar sayar da shayi ya ce yana samun rufin asiri da dan abin da yake samu daga uban gidansa.
“Da zan samu jari mai karfi, zan bude shagona na kaina.
“Amma alhamdulillah ina hadawa da wasu kananan sana’o’in domin dogaro da kaina.”
Rahotannin da Aminiya ta samu na nuna ayyukan ’yan ta’adda a Najeriya ya ragu ne sakamakon faduwar damina, da ya sanya sufuri zuwa kauyuka wahala.
Muhammad ya ce da damina hanyoyin zuwa kauyukan ba sa biyuwa, sakamakon cikar kogin Kulho da ya ratsa tsakaninsu.