Akwanakin baya ne wasu ‘Yan-fashi da suka addabi al’umar Agege suka kashe wani dansanda mai mukamin saja .
‘Yanf ashin sun samu sajan ne mai suna Obadiya Bitrus lokacin da suka shiga gidan da yake haya domin yin fashi a unguwar Saromi.
A kokarin bin diddigin yadda wannan abu ya faru mun sami zanta da wasu daga cikin wadanda suka ga faruwar wannan lamarin. Malama Zinaru daya daga cikin wadda ‘yan fashin suka shiga dakinta ta shaidawa Aminiya cewa. ‘Yan fashin sun shigar masu gidane da misalin karfe dayan dare suka dingi buga kofa da ba a budeba suka bude ta karfin tshiya nan take suka rarraba kawunansu suka dinga shiga daki bayan daki suna karbar kudade da wayoyin salula, “da suka shigo wuri na suka ce min ina kudi nace suyi hakuri ba kudi, kunga ga baba ma ya tsufa ba lafiya, sai suka kalleshi kawai suka fita.”
Zinaru tace da ‘yan fashin suka fita sai suka shiga dakin bictoria bayan fasa dakin bictoria suka karbi kudi da wayoyin salula. “Har sun fita sai suka koma dakiin nan take sai muka ji karar bindiga mun dauka ma Baban bictoria ne yayi harbin kasancewarsa dan sanda ashe su ‘yan fashin ne suka harbe shi. A gaskiya munji mutuwar sa mutumin kirkine, baya rigima kowa yabonsa ya keyi a gidan”.
Matar sajan, wadda ake kira da Mama bitoria wadda tace sunan maigidan nata Obadiya Bitrus, ta shaida mana cewa tun kafin ‘yan fahin su shiga dakin su suka jiyo su suna cewa wannan dakin Mopol ne.
Tace bayan ‘yan fashin sun fasa kofar dakinsu sai suka nemi ya basu kudi cikin fara’a yace masu zan baku kudi kuma ya dauko ya basu. Alokacin ne ‘yarsa bictoria da batafi shekara 5 ba take kururuwa tana fadawa ‘yan fashin da turanci “kar ku kashemin Baba karku kashemin Daddi”.
Bayan ya basu kudin ne suka karbi wayoyinsa suka ce kudin yayi kadan sai yace musu kudin da yake dasu kenan a gida, suka ce matar sa ma ta kawo kudi ta dakko kudin cefane ta mika musu. Har sun fita daga dakin sai wasun su suka ce su komo su kashe dan sandan nan, nan take suka juyo ko magana basu yi ba suka harbe shi a kafada suka sawa matarsa bindiga a ka suka ce in tayi kururuwa za su harbeta.
Maman bictoria ta ce “Bayan mun kai gawarsa Arewa mun binneta da muka dawo sai muka ji jita-jitar wai an kama ‘yan fashin amma har yan zu shiru ka keji ba amo ba labari, ni abin da yafi damu na shi ne nasan suwa suka kashe min miji naga kuma an gurfarnardasu a gaban koto. Munje offishin hukumar ‘yan sanda ba sau daya ba don bin bahasi amma ba wani bayani da sukayi mana. Kirana garesu shi ne in har dagaske an kama wadanda suka kasheshi to a gaggauta gurfanar dasu a gaban koto”.
Shiko abokin sagent Obadiya wanda bai so a anbaci sunansa, ya shaida mana cewa tare suka shiga aikin ‘yan sanda a shekarar 2000 a inda aka kawosu nan Legas suka zauna gida daya kafin mamacin yayi aure a shekarar 2007. Ya kara da cewa kafin mutuwar Obadiye ya na aiki ne a mopol 20 a unguwar ikeja GRA.
Ya bayyana mamacin a matsayin mutumin kirki mai son gaskiya komai dacinta a inda yai adu’ar Allah yabayyana wadanda suka kashe shi. Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda na kula da iyalan mamacin haka suma ‘yan uwa da abokan arziki na kai masu agaji.
Yadda ‘yan fashi suka yi wa wani dan sanda kisan gilla
Akwanakin baya ne wasu ‘Yan-fashi da suka addabi al’umar Agege suka kashe wani dansanda mai mukamin saja . ‘Yanf ashin sun samu sajan ne mai…