Wasu da ake zargin ’yan damfara ta intanet sun kutsa cikin asusun ajiya a banki tare da wawushe kudi Naira miliyan N523, sannan suka tura su zuwa wasu asusu 18 duk a cikin banki daya.
Mai magana da yawun ‘yan sanda na sashen yaki da masu damfara a Legas, SP Eyitayo Johnson, ya ce daga bisani ‘yan damfarar sun sake kwashe kudin suka tura a asusu sama da 200 a tsakanin bankuna 22.
- Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 7 a Borno
- Yadda ’yan gudun suka rungumi sana’ar shayi da wankin mota a Neja
Jami’in ya ce an tafka wannan sata ta intanet ne tsakanin ranar 23 da 25 ga Afrilun 2022.
Ya karada cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargin suna da hannu a aikata ta’asar.
Johnson ya ce, “Sashen ya sami izinin Babbar Kotu mai zamanta a Legas kan ya kwace N523,337,100 wanda aka kutsa cikin asusun wani kwastoma akwa kwashe sannan aka tura zuwa wasu asusu 18 duk a cikin bankin daya.
“Sannan daga bisani aka sake kwashe kudi aka tura cikin wasu asusu 225 a tsakanin bankuna 22.
“An gano N160,287,071.47 a bankuna mabambanta yayin bincike, sannan an kama mutum biyu da ake zargi da hannu a badakalar,” inji shi.