Mayakan Boko Haram da na ISWAP sun hallaka juna a wata arangama tsakanin kungiyoyin ’yan ta’addan domin kwace iko a yankin Arewa maso Gabas da Tafkin Chadi.
’Yan ta’adda da dama kuma sun samu raununka a artabun da suka yi a kauyukan Nguro da Ngoldiri da ke yankin Timbuktu Triangle a Damboa, Jihar Borno.
- Kotun Koli ta dakatar da aiwatar da wa’adin tsohuwar Naira
- ’Yan daba sun yi ta’adi a taron PDP a Gombe
Arangama ta wakana ne da misalin karfe 12 na dare a daidai lokacin da kungiyar ISWAP ta kai hari kan wasu mayakan Boko Haram da ke tafiya.
Rikicin baya-bayan nan na ranar 7 ga watan Fabrairun 2023 a Timbuktu wanda ya dauki tsawon awanni 3 ana yi, ya yi sanadin mutuwar mayaka da dama daga kungiyoyin ta’addan.
Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce mayakan Boko Haram da dama sun samu raunuka, an kuma kwace wasu tarin makamai da babura daga hannunsu.
Yayin da ake kara samun hare-hare tsakanin ISWAP da Boko Haram, an gano cewar ISWAP na shirin kaddamar da wasu hare-hare a yankin Dajin Sambisa, Marte da Abadam don kwato wasu yankuna daga Boko Haram.
A gefe guda kuma Boko Haram na yin tattaki a Dajin Sambisa da tsaunin Mandara domin fuskantar ’yan ta’addar ISWAP.
Don sake farfado da karfinta na yaki, Boko Haram ta nada wani Alhaji Ali Hajja Fusam, dan asalin Bama a matsayin sabon shugabanta a Gaizuwa, sansanin da sojojin Operation Hadin Kai suka sha lalatawa.