✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka yi wa hakimi kisan gilla a Sakkwato

A ranar Talatar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga a kan babura takwas kowane dauke da mutum uku, biyu rike da bindiga daya na tuki…

A ranar Talatar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga a kan babura takwas kowane dauke da mutum uku, biyu rike da bindiga daya na tuki suka shigo garin Balle, Hedkwatar Karamar Hukumar Gudu a Jihar Sakkwato suka yi wa Uban Kasar Balle (Hakimi), Sarkin Yamman Balle Alhaji Aliyu Ibrahim mai shekara 80 kisan gilla tare da kone mota uku ta ’yan sanda da kashe dan sanda daya da jikkata wani mutum.

Wakilinmu ya tattauna da Munzali Lukuman Balle wanda a gabansa komai ya faru, inda ya ce, “Jiya (ranar Talata) da misalin karfe 3:55 na yamma ana kiran Sallar La’asar ce ’yan bindigar suka shigo daga kauyen Bachaka garin da ya yi iyaka da Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, suka zo da babura ba mai iya cewa su nawa ne sai dai a kiyasta, wadansu su ce baburra 9 wadansu su ce 12, amma kowane babur mutum uku ne biyu rike da bindiga daya na tuka su. Farkon shigowa gari akwai wurin jami’an tsaro masu sintiri su hudu suka nufa, amma lokacin da ’yan bindigar suka iso wurin sun biyo wata motar jigila da gudu don ba su so ta riga su shiga gari, dan sanda daya aka samu a hanya, biyun suna cikin dakinsu saboda suna azumi, dayansu yana wanka. Da isarsu suka yi harbi kan motar, suka harbi fasinja daya da dan sanda.”

Munzali, ya ce kai-tsaye suka wuce ofishin ’yan sanda saboda akwai dan uwansu da ke hannun ’yan sanda kuma ana jin karbarsa ce silar zuwansu. Ya ce da ’yan sanda suka ga ’yan bindigar sai suka tsere. “Nan take suka lalata komai na ofishin suka fitar da dan uwansu suka cinna wa mota uku wuta daya ta sintiri biyu na ma’aikata kuma suka tsaya sai da motocin suka kone kurmus amma ba su sanya wa ofishin ’yan sandan wuta ba,” inji shi.

“Daga nan ne suka je gidan Sarkin Yamma ba kowa a gidan daga shi sai matarsa daya da jikansa da babban dansa da ya gudu bayan sun zo gidan. Matar gidan ta tarbe su suka tambaye ta ina Sarki ta fada musu yana cikin daki domin ba ya da lafiya, suka ce lallai yau zai warke, suka shiga cikin dakin suka same shi tare da jikansa yana karatun Kur’ani suka dakatar da karatun da jikan ke yi kuma suka yanka shi, a nan ne suka jawo Sarki a kasa har zuwa wajen gida suna magana da shi kawai sai dayansu ya harbe shi a kai a nan take ya rasu. Sun fi awa daya a cikin garin suna harbe-harbe. Mun samu labarin sun tafi da Dare (da ake zargin tsohon barawo ne) wanda wakili ne na Lakurawa wato mutanen da aka gayyato su kori barayi, yanzu muna jira ne idan Dare ya dawo to Lakurawa ne suka yi mana wannnan ta’adi, idan ko bai dawo ba, to barayin Zamfara ne suka zo,” inji shi.

“A can baya wannan yankin Tangaza da Balle na fama da barayi daga Zamfara, shi ne aka gayyato Lakurawa daga Nijar masu makamai suka tarwatsa barayin da ke yin garkuwa da mutane da tare hanya. Bayan nan sun sha alwashin duk abin da Lakurawa suka karbe musu sai sun dawo da shi,  bayan jami’an tsaron Najeriya sun kori Lakurawa tun lokacin ba wata rana da ba a tare hanya a tsakanin Tangaza zuwa Gudu, za ka yi ta ganin manyan duwatsu na tare hanya, in Magriba ta yi ba ka iya bin hanyar nan,” wata majiya ta shaida wa Aminiya.

Daya daga cikin jagororin yankin ya fada wa wakilinmu cewa, ’yan bindigar sun fada wa mutanen gari su bar gudu Sarki kawai suka zo su kashe. “Sarki yana da shekara 80 da ’ya’ya da jikoki masu yawa. Matansa uku daya ta je Sakkwato daya ta je biki lokacin da suka shigo, dayar ce kawai a gida lokacin da suka kashe shi. Da aka gan su kan babura takwas an zaci sun zo za su yi garkuwa da Sarkin ne, ko shi ma ya zaci hakan. Sai ya ce ko ba ku tafi da ni ba mutuwa zan yi. Bayan sun kashe shi suka rika yin kabbara, mutanen suna da alaka da wata kungiyar addini. Mutanen an san su ana ganin suna yawo a gari. Bai kamata a kwashe sojojin da aka kawo yankin ba,” inji shi.

Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato  Abubakar Sadik ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce suna kan bincike da zaran sun kammala za su sanar da jama’a.