✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka tayar da kauyuka 98 a Zamfara

Mataimaki Shugaban Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara, Alhaji Sani Galadima ya bayyana cewa suna cikin wani hali da suke neman agajin gaggawa. Galadima ya…

Mataimaki Shugaban Karamar Hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara, Alhaji Sani Galadima ya bayyana cewa suna cikin wani hali da suke neman agajin gaggawa.

Galadima ya bayyana hakan ne a yayin wata ganawa da Ministan Cikin Gida Laftanar Janar Abdurrahman Dambazau mai ritaya wanda ya kai ziyara ta musamman a jihar Zamfara a kokarin Gwamnatin Tarayya wajen kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

“An kai wa ’yan banga hari kuma an kashe su ranar Lahadi akan hanyarsu ta koma wa gida, bayan sun zo sun karbi kudaden da ake biyansu a nan karamar hukuma.”

Ya kara da cewa, “’yan bindigar sun kuma rubuto takarda suka aiko wa Hakimin Shinkafi cewa suna nan tafe za su kawo wa garin Shinkafi hari. Wannan mawuyacin hali da muke ciki ya kuntata mana ta yadda a kullum muna biyan miliyoyin kudi na fansa ga wadannan mahara. Muna bukatar gwamnati ta kawo mana dauki don magance mana wannan masifa.

“A halin yanzu mutane ba sa iya barci a Karamar Hukumar Shinkafi, muna bukatar gwamnati ta magance matsalar rashin yawan jami’n tsaro na ’yan sanda da na soja. A halin yanzu muna da jami’an soja 19 ne kacal a wannan Karamar Hukuma kuma muna da bukatar a agaza mana da jami’an tsaro cikin gaugawa domin yanzu mu ba mu gamsu da irin ayyukan da jami’an tsaron suke yi ba.

“Duk mun san maboyar wadannan mutane, kuma su kansu jami’an tsaron su san maboyar, amma dai abin yana daure mana kai yadda ba sa kai wa gare su. Don haka muna fatan wannan ziyara ta zamo silar waraka ga wannan matsala,” in ji shi.

Galadima ya kara da cewa kimanin kauyuka 98 ne a Karamar Hukumar Shinkafi suka yi kaura saboda matsalar hare-haren a jihar.

Da yake tofa albakacin bakinsa, Dambazau wanda kuma ya ziyarci Karamar Hukumar Anka ya bayyana cewa ya je jihar ce saboda ya gane wa idonsa yanayin tsaro a jihar. Ya kuma bayyana cewa Shugaba Buhari ya damu kwarai da halin da suke ciki.

“Wannan ba shi ne zuwa na na farko ba dangane da lamarin tsaro a wannan jiha. Shugaba Buhari ne ya turo ni don in zo mu san yadda za mu kawo karshen wannan matsala ba. Shugaban Kasa Buhari ya umarce ni da in ziyarci gundumomin Shinkafi da Anka kuma in tattauna da ku a kan wannan batu. Haka kuma yana mika ta’aziyyarsa ga wadanda aka rasa da kuma jaje ga dukiyar da aka barnata a sanadiyyar wannan tashe-tashen hankulla.”

Sarkin Shinkafi ya bayyana jin dadinsa ga wannan ziyara ta ministan sannan kuma ya kara kira ga gwamnati da ta kara kaimi wajen kawo karshen wannan masifa.