✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka tare a makarantun Zamfara

Hare-haren 'yan bindigar ya tilasta wa malamai da dalibai kaurace wa makarantun.

’Yan bindiga sun mayar da ajujuwan makarantu dakunan kwanansu a Jihar Zamfara, bayan hare-haren ’yan bindiga a sassan jihar ta tilasta rufe wasu makarantun.

Wani Shugaban Makarantar Firamare a Karamar Hukumar Birnin Magaji na jihar ya bayyana shaida wa Aminiya cewa ’yan bindiga sun taba samun su suna tsaka da karatu, suka sa ya tashi dalibai saboda suna son su kwanta su huta.

A firgice, ba tare da bata lokaci ba shugaban makarantar ya tashi dalibain ya ba su wuri domin su yi barci kamar yadda suka bukata.

Binciken da Aminiya ta yi ya kuma gano cewa hare-haren ’yan bindigar su sa an rufe makarantu a yankunan da ’yan bindigar ke cin karensu babu babbaka.

Bayan dalibai da malamai sun tsere daga yankunansu sun daina zuwa makarantun, sai ’yan bindigar suka mamaye makarantun suka mayar da su wuraren yada hakarkarinsu domin hutu.

Aminiya ta gano jiragen yaki sun kashe ’yan bindiga da dama a wani luguden da suka yi wa bata-garinbayan sun mayar da azuzuwan makarantu wuraren kwanansu a jihar.

Kazalika, akwai makarantu da dama masu fama da karancin malamai, saboda malaman na gudun zuwa makarantun kauye ko da an tura su.

Matsalar ta kai ga a hankali ana rufe makarantu saboda karancin malamai.